[[JAMB 2019]] Adadin dalibai da sukayi registan JAMB.

~Dalibai Miliyan daya da dubu dari takwas (1.8) ne Zasuyi Jamb a wannan Shekarar 
~Har Yanzu bamu sanya ranar da za’ayi Jarabawar ta Jamb ba
~Ba gaskiya bane Cewa ranar biyu ga watan March za’a fara Printing na Jamb Slip 
Hukumar Shirya Jarabawar Share fagen shiga Jami’a ta Kasa (Jamb) ta bayyana wa kafar yada labarai ta Kasa NAN a yau Alhamis a garin Legas cewa akalla dalibai Miliyan daya da dubu dari takwas (1.8) ne Zasuyi Jarabawar Jamb a wannan Shekarar ta 2019/2020. 
Idan dai ba’a manta ba an fara gudanar da yiwa dalibai Rajistar ne a ranar 10 ga watan Fabrairun 2019, kuma an dakatar da Siyar da E-Pin na Jamb din a ranar 21 ga watan na Fabrairu, yayin da shikuma Registration din aka rufe a ranar 25 ga watan Fabrairun Shekarar 2019. Mai magana da yawun Hukumar ta Jamb Dr. Fabian Benjamin yace Sunyi nasarar kammala registration din ba tare da wata matsala ba. 
Dangane da lokacin da za’a fara Printing na Jamb Slip, Dr. Benjamin ya Bukaci dalibai da suyi watsi da labarin da ake yadawa a kafafen sadarwa na zamani cewa ranar Biyu ga watan March ne za’a fara Printing din, inda ya ce wannan maganar ba gaskiya bane. 
Dr. Benjamin din ya kara da cewa Hukumar shirya Jarabawar har Yanzu bata fitar da ranar da za’a fara gudanar da Jarabawar ta Jamb ba, dan haka to bazai yuwu a fara Printing din ba har sai an fitar da ranar da za’a fara Jarabawar, Saboda ana fara Printing din ne Sati biyu kafin ranar da za’a fara Jarabawar, to kunga bazai yuwu ace za’a fara Printing ba alhali ba’a san ranar da za’a fara Jarabawar ba. 
Amma duk lokacin da Hukumar ta saka ranar farawa to zamu sanar”
Inji Dr. Fabian Benjamin, Mai Magana da Yawun Hukumar Jamb

Leave a Reply

Your email address will not be published.