[[Karanta]] Labaran Safiyar Asabar 02/03/2019CE – 25/06/1440AH.
Labaran Safiyar Asabar 02/03/2019CE – 25/06/1440AH. Cikakkun labaran
Gwamnatin tarayya za ta kafa katafaren masana’antar kera kayan jami’an tsaro a jihar Kaduna.
Fashewar bututun gas ya janyo hargitsi da tashin hankali a Bayelsa, an nemi mata da yara da dama an rasa.
Wani mutum a jihar Neja ya kashe matarsa kawai domin ta ki yarda ya kusanci shimfidarta.
Jam’iyyar APC ta dakatar da ministan ma’aikatar kula da yankin Neja Delta, Fasto Usani Usani.
Ba a taba sahihin zabe ba a Najeriya kamar na 2019 a cewar wani basarake a Benin ta jihar Edo.
Kwamitin zaman lafiya karkashin jagorancin Abdulsalami Abubakar sun gana da Shugaba Buhari a fadar shugaban kasa jiya.
‘Yan bindiga sun kashe mutane 30 a karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara.
Jiragen ruwa 15 makare da man fetir sun shigo Najeriya.
Masu amfani da yanar gizo a Najeriya sun kai miliyan 113.8 – Inji hukumar kula da sadarwa ta Najeriya, NCC.
Kasar Turkiyya ta la’anci harin da aka kai a Mogadishu.
Girgizar kasa mai karfin awo 7.1 ta a kasar Peru dake Amurka ta Kudu.
Wane Labarine Yafijan Hankalinka/Ka / ki
*Sulaiman* 👨💻