[[KARANTA]] SANIN TARIHIN MANZON ALLAH SAW

DARASI NA UKKU-(3)

TAMBAYA TA TARA
*”Waɗan su matane suka Shayar da Manzon Allah SAW??”*

AMSA
Wadda ta fara shayar da Manzon Allah SAW itace
*”THUWAIBATUL ASLAMIYYA*,mai yiwa Baffansa Abi Lahab Hidima”.
Sannan sai *HALIMATUS SA’ADIYYAH*,wadda ta tauki renonsa da shayar dashi zuwa kauyensu,ya zauna tare da ita tsawon shekara Hudu sannan ta mado da shi zuwa ga Mahaifiyarsa SAW.

TAMBAYA TA GOMA
*”Awata alqarya aka shayar da Manzon Allah SAW??”*

AMSA
“An shayar da Manzon Allah SAW a alqaryar *bani Sa’ad* kuma HALIMATUS SA’ADIYYAH  itace ta shayar da shi.

TAMBAYA TA SHA DAYA
*”Minene hikamar da Larabawa suke kai shayar da jariransu a kauyika??”*.

AMSA
“Dan kwadayin yaron ya tashi mai kuzari da ingantacciyar lafiyar jiki da gwarzantaka da jaramtaka kuma ya tashi da yaren larabci mai inganci da fusahar yarensu mafi tsada shiyasa Manzon Allah SAW idan ya fadi wani kalmar larabcin sai Sahabbbai suna mamaki yanda ya kware da fusaha na yaren sai yace ai an shayar dani a kabilar Bani Sa’ad.

TAMBAYA TA SHA BIYU
*”Wani abune yafaru lokacin da Manzon Allah SAW ake Renonsa a Bany Sa’ad??”*

AMSA
“Babban abinda ya faru shine:
*Tsaga kirjin Manzon Allah SAW *.

Daga Anas R.A yana cewa:
*”Lallai Mala’ika Jibirilu yazowa Manzon Allah SAW a lokacin yana wasa tare da yara,sai ya kamashi ya kwantar da shi ya tsaga kirjinsa ya fito da zuciyarsa ya fitar da wata yar tsoka daga cikinta,yace wannan shine rabon shaidhan a cikin zuciyarka,sannan ya wanke zuciyar acikin wata tasa ta azurfa da ruwan zam-zam sannan yacika zuciyar da aminci sannan ya mayar da zuciyar inda take kamar babu abinda ya faru,sauran yaran da suke wasa tare da shi sai sukayi maza-maza suka tafi wajan mai shayar da shi suna fada mata cewa:Lallai an kashe Muhammad……..”*
@رواه مسلم.

A wata riwayar ta Abi Na’im yana cewa:
*”….Shayarwata ta kasance a Kabilar Bany Sa’ad bn Bakar,sai na fita ni da dan wadda take shayar dani…….”*.
@رواية لأبي نعيم.

TAMBAYA TA SHA UKKU
*”Wani abu Halimatus Sa’adiyya ta aikata bayan da aka bata labarin abinda ya faru da Manzon Allah SAW??”*

AMSA
“Taji tsoron sosai sai hakan ya sanya ta mayar da Manzon Allah SAW zuwa ga mahaifiyarsa,har zuwa yakai shekara Shida.

TAMBAYA TA GOMA SHA HUDU
*”Minene hikima acikin tsaga kirjin Manzon Allah SAW??”*.

AMSA
“Acikin wannan Qassa akwai hikamar yin tattalin Manzon Allah SAW domin dacewa da amsar Wahayi daga Allah Ta’ala a nan gaba.

Tsarakewar da Allah yayi Manzon Allah SAW game cire rabon shaidhan daga cikin zuciyarsa ta yanda shaidhan yana da wata dama ta sanya wasi wasi ko rudani acikin zuciyara Manzon Allah SAW.

Wanke zuciyar da ruwan zam-zam tare da cikata da aminci da hikima wannan shine yana daga cikin falalar Manzon Allah SAW..

Allah ne mafi sani

Zamu kwana nan sai lokaci na gaba insha Allah.

Sanin tarihin Manzon Allah SAW yana cikin alamar son Manzon Allah SAW da kuma imani da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.