[[Scholarship]] Karatun course na Orthopedic kyauta a Tanzania ga yan Kano mata zallah.

Wannan scholarship ne da ake buqatar mata asalin yan kano da su cike shi, amma ga masu buqatar karantar course ba Orthopedic a Tanzania na Diploma shekaru 3.
Abubuwanda ake buqata daliba ta mallaka kafin cike wannan scholarship din sune:
1. Ya kasance tanada Credit biyar (5) tareda English Language da kuma uku daga cikin wadannan
Physics
Chemistry 
Biology 
Mathematics 
2. Ya kasance tanada JAMB mai maki sama da 180
3. Mace kawai sannan kasa da shekaru 25.
4. Ya kasance lallai yar asalin jahar kano ce. 
5. Ya kasance zata iya magana da turanci. 
Kungiyar International Committee of Red Cross (ICRC)  ne zasu dauki nauyin wannan karatun. 
Za’a tura application da kuma photocopy na takardu a ofishi da Director of Administration National Orthopedic Hospital Dala, Kano kafin ranar juma’a 8th March 2019
A taimaka a sanar da yara mata musamman wadanda sukeda abubuwanda ake buqata.

Leave a Reply

Your email address will not be published.