[[KA KARANTA]] SALLAR NAFILA KAFIN SALLAR AZZAHAR

Ya kai Dan uwa kasani,lallai bawa baya da wata hanya mafi girma da zai sami kusanci zzuwa ga Allah,da kuma samun soyayyar agareka Lamar ta hanya biyu:
*i-kokarin sauke farillar da Allah ya Dora maka*
*ii-Yawaita aiyukan nafila bayan ka sauke farilla*.
Annabi ﷺ yafi kowa aiyukan nafila kuma da kwadaitarwa.
Yawana cikin sunnar Annabi ﷺ tabbattaciya yin Sallolin nafila kafin Sallar azzhar,a lokacin da rana ta karkata daga tsakiya ana Bude kofofin Sama shiya Annabi ﷺ yake zabar wannan lokacin da yin nafila dan dacewa da wannan falala.
Annabi ﷺ ya kodaitar da my yin Nafila awannan lokacin kuma yayi hakan a aikace.
*_1-Wanda ya kiyaye raka’a hudu kafin azzahar da raka’a hudu bayanta,Allah ya haramtawa wuta cin namansa_*. 
@Ahmad Abu Dauda da Tirmizy kuma Albany ya ingantsh a Saheehut Targheeb 584.
*_2-Idan rana ta karkata daga tsakiya ana Bude duka kofofin sama,ba’a rufesu har sai an gama sallar azzahar shine nake so na dace da a dauga aiyukan alkhairin awannan lokacin_*. 
@Dhabarany ya ruwaito shi. kuma Albany ya ingantsh a Saheehut Targheeb 585
*_3-Annabi ﷺ ya kasnce yana yin Sallar raka’a hudu kafin azzahar bayan rana ta karkata daga tsakinya,yace wannan lokacine da ake Bude kofofin sama shine nake so adaukaka lokutan alkhairina zuwa sama_*. 
@ kuma Albany ya ingantsh a Saheehut Targheeb 587.
Daga Aisha Allah ya kara mata yarda,tana cewa:
Annabi ﷺ ya kasance yana yin sallar nafila raka’a hudu kafin sallar azzahar,kuma yana tsawaita tsayuwarsu kuma yana kyautata ruku’u da sujada acikinsu.
@ Albany ya ingantsh a Saheehut Targheeb 587.
*ALLAH KA SANYA MU CIKIN BAYINKA MASU YAWAITA AIYUKAN NAFILA….
Arewagist.com.ng
6th March, 2019

Leave a Reply

Your email address will not be published.