[[KARANTA]] YAWAITA ISTIGHFARI AWAJAN ZAMA DA YIN ISTIGHFARI LOKACIN TASHI DAGA WAJAN ZAMA

Iman Hasan Ibn Hasan albasari Allah yayi masa rahama yana cewa:
“Ku yawaita Istighfari a wajan zamanku da hanyoyinku da gidajenku da wajan sana’arku, domin ba kusan inda rahamar Allah zata sauka agareku ba””.
Yana cikin sunnonin Annabi SAW yawaita istighfari awajan zama kamar yadda Abdillahi dan Umar R.A yake cewa:
*”Mun kasance muna qidawa Annabi SAW awajan zaman guda yana yin istighfari sau dari yana cewa:
(ﺭﺏ ﺍﻏﻔﺮ ﻟﻲ ﻭﺗﺐ ﻋﻠﻲَّ ﺇﻧﻚ ﺃﻧﺖ ﺍﻟﺘﻮﺍﺏ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ)
*(RABBIGHFIRLI WA TUB ALAIYA INKA ANTAT TAUWABUR RAHEEM)*
@ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ ‏( 1516 ‏) ﻭﺍﺑﻦ ﻣﺎﺟﻪ ‏( 3814 ‏) ﻭﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ‏( 3434 ).
Awata riwayar acikin Musnad Imam Ahmad daga Abdillahi dan Umar R.A yana cewa:
*”Mun kasance muna qidawa Annabi s.a.w awajan zama guda yana fadar:
(ﺭﺏ ﺍﻏﻔﺮ ﻟﻲ ﻭﺗﺐ ﻋﻠﻲَّ ﺇﻧﻚ ﺃﻧﺖ ﺍﻟﺘﻮﺍﺏ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ)
*(RABBIGHFIRLI WA TUB ALAIYA INKA ANTAT TAUWABUR RAHEEM)*sau dari a wajan zama guda”
@ﻣﺴﻨﺪ ﺃﺣﻤﺪ 6/328.
Àmma zikiri ko Istighfari lokacin tashi daga wajan zama shine mutum yace:
“ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ ، ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ”.
*”SUBHANAKALLAHUMMA WABIHAMDIKA, ASHHADU AL LAILAHA ILLA ANTA ASTIGHFIRUKA WA ATUBU ILAIKA”.*
Daga Nana Aisha R.A tana cewa:
“Annabi SAW bai taba zama awajan zama ba ko yayi karatun alqurani ko yayi Sallah face sai ya rufe da wannan adduar”.
“ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ ، ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ”.
*”SUBHANAKALLAHUMMA WABIHAMDIKA, ASHHADU AL LAILAHA ILLA ANTA ASTIGHFIRUKA WA ATUBU ILAIKA”*
@ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ 3/153.
Allah bamu ikon koyi da Annabi SAW addukkan ibadun mu.
Daga
www.arewagist.com.ng
9th March 2019

Leave a Reply

Your email address will not be published.