[[Audio]] Sabuwar wakar Abba ya zama Gwamna daga bakin Sadi Sidi Sharifai

Domin sauke wannan waka, shiga nan
https://drive.google.com/file/d/1JucI3KQTCq5IYY07z2ni2Ygy4_tQ7yDu/view?usp=drivesdk

*LABARAI A TAKAICE*

*Sakamakon zaben gwamnoni  da a ka gudanar ranar 9 ga watan nan a Najeriya ya fara fitowa inda manyan jam’iiyu biyu na APC mai mulki da PDP mai adawa ke samun ragamar jihohi. Tuni a arewa maso yamma Atiku Bagudu na APC a jihar Kebbi ya samu zarcewa a karo na biyu.*

*Hakanan a jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya ya samu nasara a karo na farko bayan tsayawa takara a 2015 da PDP ta lashe a yayin da Ibrahim Dankwambo ya samu wa’adi na biyu.*

*A Lagos ma dan takarar APC Sanwo-Olu ya samu nasara kan dan takarar jam’iyyar PDP. A can kudu maso gabas Ifeanyi Egwuanyi ya samu tazarce a karakshin PDP. Hakanan Ikezie Ikpeazu ma a Abia ya samu nasarar tazarce a PDP. Akwai jihohi da alamu ke nuna wasu jam’iyyu ka iya kwacewa daga jam’iyyun da ke mulki yanzu haka a jihohin.*

*Hukumar zabe ta bayyana zaben Sokoto a matsayin wanda ba a kammala ba bayan soke zaben mazabu 136 da ke da yawan masu kada kuri’a sama da 75,000. Sakamakon da aka bayyana, Gwamna mai ci Aminu Tambuwal na PDP ne ke kan gaba da kuri’a 489,558, yayin da Ahmed Aliyu na APC ya samu kuri’a 486,145, kusan ratar kuri’a 3,413 a tsakaninsu.*

*Jami’in zabe na jihar Adamawa Farfesa Andrew Haruna ya ce zaben jihar Adamawa bai kammala ba. Baturen zaben ya ce an soke wasu zaben da aka yi a rumfuna 44 ko kuma ba a kada kuri’u a wasu wuraren ba. Ya kuma kara da cewar sun yi hakan ne saboda kuri’un da aka soke suna da yawa hakan zai yi tasiri ga masu yin takara*

*Babban jami’in zabe na jihar Kano, Farfesa Shehu Riskwa ya ce za a sanar da zaben karamar hukumar Nasarawa ta jihar Kano idan an kirga kuri’un mazabun karamar hukumar daya bayan daya. An cimma hakan ne bayan da aka kammala taron masu ruwa da tsaki, inda suka amince da hukuncin da zai kai a bayyana sakamakon zaben karamar hukumar ta Nasarawa.*

*’Yan sanda sun kama Gawuna mataimakin gwamnan Kano da kuma kwamishinan kananan hukumomi Murtala Sule Garo. Rahotanni sun ce ‘yan sanda sun kama manyan jami’an gwamnatin jihar ne bayan da suka yi kokarin tayar da rikici a Nasarawa, karamar hukumar da ta rage a kammala tattara sakamakon zaben gwamna a Kano.*

*Dan takarar jam’iyyar PRP Salihu Sagir Takai ya ba da mamaki a karamar hukumar Takai inda jam’iyyarsa ta PRP ta samu kuri’a 18,431, amma APC ce ta lashe zaben da kuri’a 19,070. Babbar jam’iyyar hamayya ta PDP ta samu kuri’a 14,119 ne.*

*Baturen zabe na jihar Filato ya bayyana zaben gwamna a matsayin wanda ba a kammala ba saboda adadin kuri’un da APC ta wuce PDP da su, ya gaza adadin kuri’un da aka soke. Yanzu za a gudanar da sabon zabe a duk rumfunan zaben da aka soken a cikin kwanaki 21.*

*Hukumar INEC ta tabbatar da Maimala Buni na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Yobe inda ya doke abokin hamayyarsa Omar Iliya na PDP. Maimala Buni ya samu jimillar kuri’a 444,013 yayin da Iliya na PDP ya samu yawan kuri’u 95,703 daga jimillar kuri’a 560 ,492 da aka kada.*

*Hukumar zaben Najeriya ta dakatar da ci gaba da lamuran zabe ko sakamakon zabe daga jihar Rivers a kudu maso kudancin Najeriya. Matakin ya biyo bayan hargitsi da a ka samu ciki kuwa har da bayanan da ke nuna batar dabo da shugaban hukumar zabe na kasa a jihar ya yi.*

*Hukumar zaben INEC ta ce yanzu ta kafa kwamitin masu bincike don gano dalilin samun cikas din kuma su kawo rahoton su a nan da sa’a 48.*

*A na cigaba da juyayi kan hatsarin jirgin saman Habasha da ke dauke da fasinjoji 157 da duk su ka riga mu gidan gaskiya. Jirgin dai ya tashi daga Addis Ababa zuwa babban birnin Kenya Nairobi inda kan hanyar sa ya samu hatsarin mai munin gaske.*

*Cikin fasinjoin akwai ‘yan Kenya, habasha,Burtaniya da ma ‘yan Najeriya wadanda ba sa rike da takardun tafiya na kasar. Wasu daga ‘yan uwan wadanda ke cikin jirgin sun taru a filin jirgin sama a Nairobi don tarbar fasinjoin inda wannan labari ya zo mu su.*

*‘Yan Najeriyar biyu sun hada da Farfesa Pius Adesanmi da ke dauke da FASFO na kasar Kanada da Ambasada Abiodum Bashua da ke dauke da FASFO na majalisar dinkin duniya.*

*Ibrahim Baba Suleiman*
*Jibwis Social Media Media*                                                                         *04-Rajab-1440*
*11-March-2019*

arewagist.com.ng

Leave a Reply

Your email address will not be published.