Kalaman dan takaran Gwamnan Gombe na PDP bayan ya fadi zabe. Zaka yi mamakin abinda yace.

Assalamu Alaikum
Ina so inyi amfani da wannan kafa domin na mika sakon godiya ga dukkan masoya na, shugabannin jamiya, yan uwana, alummar jahar Gombe dama dukkan wa’inda suka goyi bayana daga jahar Gombe dama wa’inda suka goyi baya na daga wasu jahohi da dukiyoyinsu, karfinsu da adduo’i a matsayin Gwamna jahar Gombe a shekarar 2019 wanda Allah bai kaddare mu da nasaran cin zabe ba.
Wannan hukunci rashin cin zabe da Allah ya aiko mana, mun karbe sa hannu bibbiyu kuma mun masa godiya akai.
Nayi takaran kujerun siyasa sau shida a baya Allah duk ya bani nasara, a wannan takarkari da nayi kuma ba’a taba kaini kotu ba bayan zabukan, to don haka nida jamiyata baza muje kotu ba akan sakamakon zabe. Mun yarda  da hukuncin Allah.
Wanda suka ci Allah ya basu sa’an cika alkawura da suka dauka da ikon ciyar da jahar Gombe gaba, wannan shine burin mu kuma shi ya kwadaitar damu muyi takara.
Yayi yakin neman zabe watakila na batawa wani rai to ina neman afuwa banyi haka ba don in bata mai rai ba sai don inci zabe. Allah ya gafarta mana gaba daya.
Maganan takara da jama’a suke kara tun tubarmu wannan lokaci ne kawai zai tabbatar da haka. Allah ya zabar mana da mafi alkairi ako da yaushe.
Zancigaba da taimakawa alummar jahar Gombe, duk abunda muka ga zai kawo wa jahar Gombe cigaba zamuyi iyakar kokarin mu muga mun kawo da yardan Allah.
Magoya bayana nagode muku sosai da soyayya da kuka nuna min ina farin ciki da haka sosai Allah ya zabar mana da mafificin alkairi a ko da yaushe.

Leave a Reply

Your email address will not be published.