[[Karanta]] Zuwa yanzu Gwamnoni 22 ne aka sanar da cin zaben su.

An samu sabbin Gwamnoni biyo bayan zaben da aka gabatar a ranar asabar da ta gabata a jahohi 29.

Hukumar mai zaman kanta wato INEC ta sanar da Gwamnoni 20 wadanda sukayi nasaran lashe zabe.

Gwamnoni 9 zuwa yanzu ba’a fadi matsayin zaben su ba. Sannan INEC ta tabbatar da cewa sakamakon jahaohi 5 da ba’a kammala ba wato “inconclusive”. Wadannan jahohi sune
Bauchi
Benue
Sokoto
Adamawa da
Plateau.

Sannan zaben jahar Rivers an janye shi gaba daya wato baza’a yi ba kwata kwata ba yanzu.

Ana jiran sakamakon Jahar Kano ganin cewa an kammala tattara sakamakon, kawai sai INEC ta saka jahar Kano cikin jerin jahohin da ba’a kammala ba wato “inconclusive” duk da cewa dan takarar PDP ya baiwa dan takarar APC tazara a karshen sakamakon.

A safiyar yau ne kuma tsohon mataimakin Speaker na Green Chamber wato Rt. Hon. Emeka Ihedioha aka tabbatar dashi a matsayin wanda ya lashe jahar Imo a matsayin Gwamna.

Sannan a jahar Taraba, shi gwamna mai ci shine aka tabbatar a matsayin wanda ya lashe zaben, hakan shine ya tabbatar da jimilar gwamnoni 22 wadanda aka sanar a fadin kasar Nigeria.

Ba’a yi zaben Gwamnoni  a jahohi 7 ba, jahohin sun hada da
Edo
Kogi
Ondo
Ekiti
Anambra
Osun
Bayelsa.

Ga kuma sunayen Gwamnonin guda 22 akasa.

Kuna samun wannan labari ne daga shafin arewagist.com.ng

Leave a Reply

Your email address will not be published.