[[JAMB 2019]] Kididdigar Daliban da Suka nemi gurbin Karatu a kowanne Faculty a Kakar karatu ta shekarar 2019/2020, daga Hukumar Jamb.

~Kididdigar Daliban da Suka nemi gurbin Karatu a kowanne Faculty a Kakar karatu ta shekarar 2019/2020, daga Hukumar Jamb. 
Hukumar Shirya Jarabawar Share fagen shiga Jami’a ta Kasa (Jamb) ta fitar da Kididdigar daliban da suka nemi gurbin karatu (Admission) a Kakar karatu ta shekarar 2019, dogaro da kowanne Faculty a matakin Degree da kuma matakin Diploma. Kazalika wannan Kididdigar bawai ta Jami’a daya bane, a’a na duka daliban da zasuyi Jamb ne a wannan Shekarar, da fatar Allah ya bawa mai rabo sa’a. 
Ga Kididdigar Kamar Haka a matakin Degree:-
1. Faculty Of Administration:-
Dalibai mata Kimanin dubu tamanin da bakwai da dari shida da talatin da biyar ne (87,635) suka nemi admission a wannan bangaren na Administration, a yayin da kuma dalibai maza kimanin dubu Saba’in da takwas da dari bakwai da goma Sha uku ne (72,713) suka nemi admission a administration din. Jimillar su ya kama Dubu dari da Sittin da shida da dari uku da Arba’in da takwas (166,348)
2. Faculty Of Agriculture:-
Dalibai mata dubu goma sha hudu da dari biyar da tamanin da shida ne (14,586) suka nemi admission a bangaren, inda kuma dalibai maza yawan su yakai Dubu goma Sha takwas da dari daya da Arba’in da uku (18,143) 
Jimillar su ya kama Dubu talatin da biyu da dari bakwai da Ashirin da tara (32,729)
3. Faculty Of Art And Humanities:-
Akwai adadin dalibai mata Dubu Hamsin da bakwai da dari biyu da goma Sha Biyar (57,215) da suka nemi gurbin karatu a bangaren, inda su kuma dalibai maza adadin su ya kai dubu Hamsin da daya da dari biyar da tis’in da hudu (51,594)
Jimillar su ya kama Dubu dari da takwas da dari takwas da tara (108,809)
4. Faculty Of Education:-
Yanada adadin dalibai mata Dubu Hamsin da daya da dari biyar da Arba’in da takwas (51,548) da suke burin ganin sun samu gurbin karatu a Jami’a
A Yayin da su kuma dalibai maza adadin su ya kai dubu talatin da tara da dari uku da hamsin (39,350)
Jimillar su ya kama Dubu tis’in da dari takwas da tis’in da takwas (90,898)
5. Faculty Of Engineering/Tech/Env:-
Akwai adadin dalibai mata Dubu Ashirin da dari biyu da hamsin da shida (20,256) da sukeda burin zama Injiniyoyi
Inda su kuma maza yawan su ya kai Dubu dari da tamanin da takwas da dari shida da Saba’in da shida (188,676)
Jimillar su ya kama Dubu dari biyu da takwas da dari tara da talatin da biyu (208,932)
6. Faculty Of Law/Legal Studies:-
Facultyn Yayi farin jinin samun dalibai mata Dubu Hamsin da takwas da tis’in da uku (58,093) da suke burin zama lauyoyi
Inda kuma dalibai maza adadin su ya kai Dubu Arba’in da hudu da dari takwas da Sittin da takwas (44,868)
Jimillar su ya kama Dubu dari da biyu da dari tara da sittin da daya (102,961)
7. Faculty Of Med/Pharm/Health Sciences:-
Dalibai mata Dubu dari biyu da Saba’in da biyar da dari uku da Ashirin da uku ne (275,323) suka nemi admission a wannan bangaren, a yayin da kuma dalibai maza adadin su ya kai Dubu dari da sittin da dari biyar da Saba’in da hudu (160,574)
Jimillar su kuma ya kama Dubu dari hudu da talatin da biyar da dari takwas da tis’in da bakwai (435,897)
8. Faculty Of Sciences:-
Bangaren Sciences Kuma ya samu dalibai mata Dubu dari da hudu da dari hudu da Arba’in da biyar (104,445), inda kuma dalibai maza adadin su ya kai Dubu dari da Saba’in da shida da dari uku da talatin da biyar (176,335)
A Yayin da Jimillar su ya kai Dubu dari biyu da tamanin, da dari bakwai da tamanin (280,780)
9. Faculty Of Social Sciences:-
Yanada Dalibai mata Dubu dari da sittin da biyu da dari tara da goma Sha uku (162,913) da suke neman admission a wannan tsangayar, a yayin da kuma dalibai maza adadin su ya kai Dubu dari biyu da goma Sha uku da dari hudu da Saba’in da biyar (213,475)
A Yayin da Jimillar su ya kama Dubu dari uku da Saba’in da shida, da dari uku da tamanin da takwas (376,388)

Daga arewagist.com.ng

Leave a Reply

Your email address will not be published.