[[JAMB/INEC]] An kara Samun Clashing Tsakanin Hukumar Jamb da Hukumar INEC.

~An kara Samun Clashing Tsakanin Hukumar Jamb da Hukumar INEC 
Hukumar Shirya Jarabawar Share fagen shiga Jami’a ta Kasa (Jamb) ta kara Samun Clashing tsakanin ta da Hukumar Shirya zabuka ta kasa Mai zaman kanta (INEC). 
Idan ba’a manta ba Hukumar ta Jamb ta sanya ranar 16 ga watan March zuwa ranar 23 ga watan dai na March a matsayin ranakun da za’a gudanar da Jarabawar, inda ita kuma Hukumar INEC ta sanya ranar 23 ga watan February da ranar 2 ga watan March a matsayin ranakun da za’a gudanar da babban zaben kasar da kuma na gwamnoni da ‘yan majlisu, kwatsam sai Hukumar ta INEC ta bada sanarwar dage zabukan, inda ta sanya ranar 23 ga watan February da ranar 9 ga watan March a matsayin Sababbin ranakun da za’a gudanar da zabukan. 
Dan haka, hakan ya tilasta wa Hukumar ta Jamb canja ranar da za’a gudanar da Jarabawar ta Jamb wanda kuma har yanzu bata saka wata ranar ba, a yayin da kuma ta canja ranar da za’a gudanar da Jarabawar ta mock zuwa ranar 23 ga wannan watan na March, Kwatsam kuma sai gashi Hukumar ta INEC ta sanya ranar 23 ga watan na March a matsayin ranar da za’a canja zaben wasu wurare acikin wasu Jihohin da aka gudanar da zaben.
Jihohin sun hada da: Adamawa, Kano, Bauchi, Benue, Plateau da kuma Sokoto saidai kuma har yanzu Hukumar ta Jamb batace komai ba akan batun, Shin zata Kara daga Jarabawar ta Mock ne Saboda wadannan Jihohi guda 6 ko kuwa ya zatayi, yanzu dai ita muke Sauraro. 
Idan ba’a manta ba daman Hukumar ta Jamb tace bazata saka ranar da za’a fara Printing na Jamb Slip ba, ko kuma ranar da za’a gudanar da Jarabawar ta Jamb har sai bayan an kammala zabukan kasar, Saboda bataso ta saka ranar dan kar tayi Clashing da ranar zabe, to amma kuma duk da haka gashi bata tsere ma hakan ba.
Daga Arewagist.com.ng

Leave a Reply

Your email address will not be published.