[[KA KARANTA]] LADUBBAN SALLAH DA HAƘIƘANIN YANDA AKE SALLAH.

LADUBBAN SALLAH DA HAƘIƘANIN YANDA AKE YINTA:
Alƙali Imam Abu Yusuf shi ne babban almajirin Imam Abuhanifa wanda shi ne jagoran mazhabar Hanafiyya.. Wata rana ya ji labarin wani bawan Allah Sufi, matashi mai suna Hatimul Asam da yake bayar da karatu a wani Masallaci akan zuhudu  da gudun duniya, sai Alƙali Abu Yusuf ya ce wa almajiransa: ku tashi mu tafi wurinsa, mu yi masa wasu ƴan tambayoyi, idan amsoshinsa sun yi mana, sai mu zauna mu ƙaru.. Da suka shiga Masallacin sai ya tambaye shi: ya kai wannan matashi, yi mana magana akan sallah? Sai Hatimul Asam ya ce: ladubban sallah kake tambaya, ko kuwa haƙiƙanin yanda ake yinta?
Sai Alƙali Abu Yusuf ya yi mamaki a cikin zuciyarsa na cewa: mun yi masa tambaya ɗaya, shi kuma ya mayar da ita tambayoyi biyu..
To faɗa mana ladubbanta, sai Hayimul Asam ya ce: ladubbanta su ne: ka tashi bayan ka suranta umurnin Allah akan a yi sallah, sannan ka yi tafiya kana mai neman lada a wurin Allah, ka fara sallar bayan ka ɗaura niyya, sannan ka yi kabbarar harma cikin girmama Allah, ka yi karatun sallah a tsanake, ka yi ruku’i cikin tsoron Allah, ka kuma yi sujada cikin ƙasƙantar da kai, ka yi tahiya cikin ikhlasi, sannan ka yi sallama kana mai haɗa sallamar da rahamar Allah..
Sai Abu Yusuf ya ce: yaya kuma haƙiƙaninta yake?
Sai Hatimul Asam ya ce: Ka sanya Ka’aba a gabanka, kaman kana kallon ma’aunin da ake auna ayyuka, ka hararo kanka a kan siraɗi, ga aljanna a damanka, ga wuta kuma tana hagunka, ga kuma mala’ikan mutuwa yana nemanka, sannan duka bayan haka, ba ka san shin an amshi sallar taka, ko ba a amsa ba..
Sai Alƙali Abu Yusuf ya ce: tun yaushe kake yin irin wannan sallar? Sai Hatimul Asam ya ce: shekaru ashirin da suka wuce.. 
Sai Alƙali Abu Yusuf ya juyo ya ce da almajiransa: ku tashi mu rama sallolin shekaru hamsin da suka wuce…
Ya Allah Ubangiji ka sanya mu cikin bayinka masu yin sallah kaman yanda ta kamata, ka kuma gafarta mana gazawar da muka yi… Allahumma amin..
Saleh Kaura
Daga arewagist.com.ng

Leave a Reply

Your email address will not be published.