[[Ka karanta]] Wuraren da za’a sake zabe a Jahar ADAMAWA.

Hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC ta sanar da cewa wannan zabe da za’a sakeyi a ran 23th March, 2019 a jahar Adamawa za’a yi ne a kananan hukumomi 14 na fadin jahar. 
Shugaban INEC na jahar Mr. Kasim Gaidam shine ya sanar da hakan a ranar lahadi da ta gabata wa “News Agency of Nigeri” (NAN).
Gaidam yace zabukan za’a yi ne a gundumomi (wards)  29 da kuma mazabu (polling units)  44 saboda kuri’u 40,000 da aka soke a lokacinda aka gabatarda zaben Gwamna wanda ya gabata. 
Hukumar INEC ta shirya gabatar da wannan sauran zaben a fadin jahar. Zaben zai gudana ne a kananan hukumomi 14, gundumomi 29 da kuma mazabu 44.
Gaidam yace za’a yi wannan zaben ne a kananan hukumomi kamar haka: Yola South,  Fufore, Ganye, Girei, Guyuk da kuma Hong. 
Sauran kuma sune: Lamurde, Numan, Madagali, Michika, Mubi North, Shelleng, Song da kuma Toungo. 
Gaidam yace an sanarda zaben ne a matsayin wanda ba’a kammala ba (inconclusive) saboda haka doka ta tanadar,  ta hanyar yawan katin zabe da aka yanka, ba wadanda aka karba ko aka tantance ba. 
Yace duk wasu sakamakon zabe dake yawo a dauke a matsayin kanzon kurege matukar ba hukumar INEC bane ta sanar. 
Idan baku manta ba, ma’aikacin INEC Prof. Andrew Haruna ya nuna cewa dan takarar jam’iyyar PDP, Adamu Fintiri ya samu 367,472, sannan shi Gwamna mai ci Muhammadu Bindow ya samu 334,995.
Tazaran dake tsakaninsu 32,476.
Kuna samun wannan labaru ne daga www.arewagist.com.ng

Leave a Reply

Your email address will not be published.