[[KI KARANTA]] MATA GA HANYA MAI SAUKIN ZUWA ALJANNA AGAREKU.

Mata ku kiyaye abubuwa guda Hudu zaku shiga aljanna:
*1-Kiyaye Sallolin farillaar guda biyar*.
Kiyaye sallah yana nufin abubuwa guda hudu:-
-Yin Sallar irinta Annabi SAW.
-Yinta acikin lokacinka musammamma afarkon lokacinta
-Cika Sallar kuma da jirantasu yadda Allah yayi umarni.
-Kyautata rukunanta da yinta abisa ilimi da ikhalasy.
*2-Yin Azumin watan Ramadan*.
Da kuma kokarin yin na nafila dan yacike gurbin na farillah.
*3-Kuma tayi biyayya ga mijinta*.
Biyayya ga miji yana nufin:
-Aikata dukkan abinda miji yayi maki umarni matukar bai sabawa umarnin Allah da na
manzonsa ba.
-Hanuwa da abinda yayi maki hani matuqar bai ci Karo da na Allah da Manzonsa ba.
-Barin dukkan abinda zai bata masa rai da kuma bashi dukkan wani hakkinsa da yake
kanki.
-Fifita matsayinsa akan na kowa in ba Allah da Manzonsa ba.
*4-Kiyaye farjinta*.
Bata zina ko Nemin mace yar’uwarta ko biyama kanta da kanta buqata.
Annabi SAW yana cewa:
*”Idan mace ta Sallaci Sallolinta biyar na farillah,Tayi azumin watanta na farillah(Ramadan)*.
Tayi dha’a ga mijinta kuma ta kiyaye firjinta,za’ace da ita:
Shiga aljanna ta Inda kikaga dama”.
@Ahmad-1664
@Albany ya ingantasa
@Duba: Jami’i-660.
*Allah kaba iyayanmu mata musulmai ikon kiyaye wandanan abubuwa guda hudu amin*.
Daga arewagist.com.ng

Leave a Reply

Your email address will not be published.