[[KA KARANTA]] DAGA CIKIN KURA KURAN MAI SALLAH 02

DAGA CIKIN KUSA-KUREN MAI SALLAH

DARASI NA BIYU-(2)

KUSKURE NA HAƊU?
*Rashin ɗaga hannaye a wajen da Sunnah ta keɓe da ɗaga hannu acikin sallah*.

ABINDA YAKE DAIDAI
{Manzon Allah SAW yana ya kasance yana ɗaga hannuwa acikin sallah a waje kamar haka:-
*_Lokacin kabbarar Harama_*

*_Lokacin yin ruku’u da lokacin ɗagowa daga ruku’u_*.

*_Da lokacin tashi daga Tahiyar farko_*

*_Wani lokacin yana ɗagawa lokacin yin sujada_*.

KUSKURE NA BIYAR
*5-Wasu daga cikin masu sallah suna ɗora hannunsu na dama akan na Hagu a Samar cibiyar su ko kan cikin su*

ABINDA YAKE DAIDAI
{Shine mutum ya ɗora hannunsa na dama akan na hagu a kan ƙirjinsa wajen ɓangaran dama ko Hagu}

KUSKURE NA SHIDA
*6-Rashin tsayar da gani waje guda acikin sallah da rashin tsayar da kallo ga wajen Sujada acikin sallah*

ABINDA YAKE DAIDAI
{Abin da Sunnah ta koya game da inda ganin mai salla zai kasance shine:-
*Idan yana tsaye ko ruku’u ko tsakanin sujada guda biyu to zai mayar da kallonsa zuwa ga inda yake yin Sujada*.

*Idan kuma yana zaman Tahiya ta farko ko ta biyu, to zai mayar da kallonsa ne zuwa ga ɗan yatsarsa manuniya*.

*Idan kuma yana kusa da Liman to idan yana tsayene to zai kalli liman*.
@ﺳﻤﺎﺣﺔ ﺍﻟﺸﻴﺦ / ﻋﺒﺪﺍﻟﻌﺰﻳﺰ ﺑﻦ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﺑﺎﺯ ‏] ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ
‏@ﻓﻀﻴﻠﺔ ﺍﻟﺸﻴﺦ / ﻣﺤﻤﺪ ﺑﻦ ﺻﺎﻟﺢ ﺍﻟﻌﺜﻴﻤﻴﻦ ‏] ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ
‏@ﻓﻀﻴﻠﺔ ﺍﻟﺸﻴﺦ / ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻋﺒﺪﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺠﺒﺮﻳﻦ ‏] ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ
‏@ﻓﻀﻴﻠﺔ ﺍﻟﺸﻴﺦ / ﺻﺎﻟﺢ ﺑﻦ ﻓﻮﺯﺍﻥ ﺍﻟﻔﻮﺯﺍﻥ ‏] ﺣﻔﻈﻪ ﺍﻟﻠﻪ
@ﻭﺍﻟﻠﺠﻨﺔ ﺍﻟﺪﺍﺋﻤﺔ ﻟﻺﻓﺘﺎﺀ
ﺟﺰﺍﻫﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻦ ﺍﻹﺳﻼﻡ ﻭﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ ﺧﻴﺮ ﺍﻟﺠﺰﺍ

   Allah ne mafi sani

Allah ya bamu ikon gyarawa,mu haɗu a Darasi na gaba insha Allah

Leave a Reply

Your email address will not be published.