[[KARANTA]] SAKO ZUWA GA AL’UMMAR KANO.

SAKO ZUWA GA AL’UMMAR KANO.
COMMISSIONER OF POLICE KANO (CP WAKILI)
NA GA YIN SHIRUN BASHI DA MA’ANA.
A ‘Yan kwanakin da suka gabata ne Jihar Kano mai dumbin al’umma, tarin dukiya, arziki da kasuwanci, da uwa uba harkoki na ilimin addini da na zamani, ta yi sabon Ango a matsayin Kwamashinan Yan sanda na Jihar, mai suna Malam Muhammad Wakili.
Zuwan wannan bawan Allah Ya haifarwa da Jihar ta Kano mai albarka D’a mai ido, domin ko Shaidan sai da ya girgiza da zuwan sa!!! A cikin ‘Yan kwanaki kalilan an samu cigaba masu yawa da ba a taba samun makamantansu ba tsawon shekaru, an yi kokari matuka wajen dakile harkokin: Daba, Sara-suka, Bangar siyasa, Fashi da makami, da uwa uba harkokin shaye-shaye da fataucin miyagun kwayoyi.
Hakika al’ummar Jihar Kano, masu yi mata fatan alkhairi, masu kaunar zaman lafiya, masu kaunar cigaba na fili da na boye,masu kaifin basira, wadanda basu cusa son rai, kwadayi, goyon bayan zalunci a tattare da su ba, kullum babu komai a zukatansu da kalaman su da alkalumansu sai tsantsan nuna so da kauna da fatan alkhairi ga sabon kwamashinan namu CP WAKILI.
Wadanda kuma suke da wata manufa maras kyau,suke mummunan fata ga Jihar Kano ko sun sani ko basu sani ba, suna adawa da kiyayya ga CP WAKILI saboda wasu manufofi nasu.
A ‘Yan kwanakin nan ne dai wasu rubuce-rubuce, da maganganu suka baza kafafen sada zumunta na zamani, inda suke bayyana suka karara ga CP WAKILI da nuna zargi a gare shi cewa yana goyon bayan wata Jam’iyya ta siyasa ne, yana musu aiki.(Magana ce ta karya maras gindin zama a zukata nagari)
MASU ADAWA DA CP WAKILI:
A iya hasashe na, masu nuna adawa da jefa wancan zargi maras tushe ga CP WAKILI, zasu iya zama kamar haka:
(1) Bangaren Gwamnatin Kano: Gwamnati da ‘Yan barandan ta, masu goya mata baya ta kowacce fuska suna nuna adawa da zargi da tuhuma ga CP WAKILI saboda sabon abu ya zo musu. Adalci mai kore zalunci ya bayyana, haske maganin duhu ya haskaka sararin Jihar Kano, domin ba boyayyen abu bane a baya, irin yadda aka yi amfani da Jami’an Yan sanda wajen cin kare babu babbaka, ma’abota Gwamnati suka aikata abinda suke so, suka yi ta aikata nau’uka iri-iri na zalunci, danniya, da duk wasu munanan abubuwa, kuma suka samu kariya da daurin gindi daga Kwamishinan Yan Sanda da ya gabata, idan kana APC, idan kana tare da Gwamnatin Kano to zaka ci karen ka danye, ka yi abinda kake so, babu abinda zai sameka.
A yayin da CP WAKILI yazo Kano, sai ya nuna wancan lokaci fa ya wuce,!! ya zama (Khabaru kaana) shi aiki yazo yi tsakani da Allah a Jihar Kano, babu ruwansa da Gwamna,Gwamna bai isa ya sashi zalunci ko danniya ba, kowa yayi aikinsa da gaskiya, kudi, cin hanci, alfarma, kusanci da Gwamna duk basa gabansa, saboda haka duk wanda ya taka doka to doka zata murtsuke shi! Ba dan APC, ba dan PDP, ba dan PRP, ba dan komai!! kowa abin yiwa hukunci ne idan ya taka doka.
Wannan sai ya bayu zuwa ga bangaren Gwamnati da Yan barandansu suka kulla kiyayya da gaba da adawa mai karfi ga CP WAKILI, suka tsane shi kamar yadda tsuntsaye suka tsani mujiya! Koma sama da haka, ana ambatarsa sai suji gaban su ya ce: “RAAAS!”, sai suka fara zaginsa da cin zarafinsa da watsa rubuce-rubuce na son rai. Domin dai ya toshe wadancan kofofi na kama-karya, danniya,da amfanin da karfin iko wajen yin abinda aka ga dama mara kyau.
(2) Bangare na biyu: Sune masu tsananin adawa ga Engr. Rabiu Kwankwaso, ko ga Jam’iyyar PDP, wadda tsantsar adawarsu har ta kai su ga yiwa Jihar Kano mummunan fata, har ta ingizasu ga kada ayi adalci ga bangaren PDP, ko Kwankwaso, su a san ransu tunda suna adawa da Kwankwaso, tunda basa son PDP, to CP WAKILI ya sakarwa APC, ya rabu da Ganduje da Yan barandansa su cigaba da cin karensu babu babbaka a Jihar Kano, a tauye hakkin duk wani mai hakki indai ya fito daga bangaren Kwankwaso ne, daga PDP tayi wani abu sai su chanza masa zani, suna sanyawa zukatansu sun aikata laifi azo a kama su! Ayi musu kaza. Wadda wannan kuskure ne. Kuma basu nemawa Jihar Kano alheri ba. Adawarku ya kamata ta takaita ga Kwankwasi, ko PDP.
NB: Adawa da Kwankwaso: Akwai masu yinta bisa gaskiya, bisa daidai, saboda yadda ya fito a kwanaki yaci mutuncin addini, ya tafka babban kuskure mummuna. Amma duk da haka a tsaya iya Kwankwaso da maganganun sa, kada hakan ya kai ga son zalunci ko kin tabbatar da adalci da kin tsayar da doka da oda. Idan Kano ta rikice ta lalace Matasa suka afkawa shaye-shaye aka fara zubda jini, aka rufe makarantu da kasuwanni da asibitoci, shi Kwankwaso ma guduwa Kasar waje zaiyi. Kune dai a garin da Iyayenku da Iyalanku.
(3) Mutane na uku da na hudu: Sune wasu mugaye kawai, wasu kuma dolaye wadanda basa fatan a samar da adalci, su Kano ma ta yamutse babu ruwansu, inma dai saboda mugun nufi, wasu kuma saboda sakarci basu san inda yake musu ciwo ba, saboda haka sai suka goyi bayan ayi adawa da CP WAKILI, a yi masa karerayi, a munana masa zato.
(5) Watakila mutane na biyar; Sune wadanda su har ga Allah a iya ganin su da hangensu CP WAKILI yana goyon bayan wasu Jama’a ne, (Amma irin wadannan sanin su da al’amuran yau da kullum, bibiyar su da abubuwan dake wakana, kaifin basirarsu, ma’aunan awon su suna da rauni)
– ABUBUWANDA AKE ZARGIN CP WAKILI DASU.
(1) Ya kama Dan Majalisar Kiru da Bebeji Abdulmumin Kofa, bai kama tsagin PDP ba: Rikici ne ya afku a garin Kofa dake Bebeji, CP WAKILI a karon farko zai yi amfani da rahoton Baturen Yan sanda na Karamar hukumar (D.P.O), sannan kuma a dokance CP WAKILI PDP ta nemi izini a wajensa, bisa tanadin doka ya sahhale mata gudanar da taro a garin, APC ta nema ya hanata bisa tanadin doka, domin PDP ta rigasu kuma an riga an bata dama,amma APC bata yadda ba, tayi tsammanin irin Kwamashinan Yan Sanda ne na baya, sai tayi kunnen Uwar shegu, taje ta tanadi mafarauta da Yan sara suka suka shirya takalar rikici,A karon farko suka afkawa PDP,su kuma PDP an daukesu ne a matsayin masu kare kai “DEFENDERS” (Ko da kuwa sun wuce gona da iri idan an yi bincike bamu sani ba, kuma hukunci na gaskiya da tsantsar adalci sai a gaban masanin fili da boye, ranar da hannaye, idanuwa, bakuna da kafafuwa zasu bayar da shaida)
(2) CP WAKILI ya kama Mataimakin Gwamna: E mataimakin Gwamna bai ja girmansa ba, amma tunda ance yana da kariya (Immunity) a section (308) to shima CP WAKILI yace ba kamashi yayi ba, kariya ya bashi don gudun kada wani abu ya same shi daga al’ummar gari masu kishin kansu. Gashi kuwa:
الحكم بالظاهر  والله يتولى السرائر ( النووي في المنهاج)
A na hukuci ne da abinda yake a fili asarari, Allah Shi ne masanin abinda ke boye.
(3) Yana goyon bayan PDP, Ya bar Kwankwaso yana abinda yaga dama ba a kama shi ba: Wannan shine mafi raunin zargi akan CP WAKILI! Don Allah me PDP tayi ba a dauki matakin da ya kamata ba? Cewa nake ranar da Atiku Abubakar yazo kano Campaign sai da CP WAKILI ya kama matasa Yan PDP sama da mutum (500) yayi holansu a cibiyar rundunar Yan Sanda na Jihar Kano Yan jaridu suka dauki hotuna suka watsa duniya, aka yi hira dashi yace kada wanda ya sake yazo neman bail nasu, zai toshe shi ma idan yazo. Kuma har zuwa yau a iya sanina ba a sake su ba. Duk kuwa abinda ake ganin PDP ko Kwankwaso sun aikata an daga musu kafa ba dauki mataki akan haka ba, to APC magoya bayan Ganduje sun aikata sama dashi suma shiru!!!
Sai Kalaman Kwankwaso na cewa: “Kowa Security” wannan za a iya yi masa fassara da dama, ba lalle kai tsaye yana nuna neman tayar da fitina ba, ita kanta hukumar Yan sanda tana cewa kowa ya zamto Security, ya sa ido ya bawa hukuma rahoto, kuma mafi munin irin wadannan kalamai sun gabata, kuma ana ci gaba da watsa su daga bakin Shugaban APC na Kano Abdullahi Abbas, shima fa har yanzu ba a kama shi ba. Idan kuma har kalaman Kwankkwaso a zahiri suna nuna rikici ko neman tarzoma, kuma ba a dauki matakin da ya kamata akansa ba (to anyi sakaci) amma sai a hada su da na Yan APC, kuma dai aikin Dan adam ne dole sai an samu gajiyawa. Amma wannan bai kai ga kuzo kuna goyon bayan wasu mugayen mutane da suke so a sakar musu mara su yi ta’addanci, zalunci, danniya ba, ku zo kuna taimaka musu akan Mutumin da yake kokarin ceto muku: Garinku, Matasanku.
(4) Akwai batun Kama Lauyoyi, to CP WAKILI jiya yaje Ofishin Kungiyar Lauyoyi ya basu hakuri, sun fahimci juna, ya nuna yayi kuskure. Wannan ya rufe bakin duk mai nemab gaskiya, sai kuma ku bari gaba idan ya maimaita sai ku zage shi.
A HANKALCE:
(A) Yanzu mutumin da bai bi bangaren Gwamnati da suke da karfin mulki sama da kasa, suke da lalita cike da dumbin kudade, suke da mafi karfin zaton sake komawa mulki (a duniyance) shi ne kuma zai bi PDP!!! Me zasu bashi? Me zasu tare masa? Haba mai hankali!!! A dai duba.
(2) Yanzu mutumin da yazo zai taimaki Jihar Kano, mutumin da ya fara irin wannan namijin kokarin a Kano, don an samu wasu kura-kurai (idan ma sun tabbata)  shine zaku goyi bayan wadanda ya hana zalunci, suka fito suna zarginsa, ku taimaka musu wajen shatale namijin kokarinsa? Kano fa ya taimaka, Matasanku ya nunawa kauna, adalci fa yake kokarin kamantawa.
(3) A hankalce masu hikma sun ce: Duk Jami’in tsaron da kaga basa shiri da Gwamnati mai ci, suna zaginsa suna aibantashi, to mai gaskiya ne, tsayayye ne akan aikinsa, yaki bayar da kai bori ya hau ne.
NI DAI:
Koda wadancan abubuwa sun tabbata akan CP WAKILI , to ina tare dashi wajen kokarin da yake yi ga Jihar Kano, ina yi masa fatan alkhairi, ina kaunarsa, ina kuma yi masa adduar nasara, wadancan kura-kuran kuma idan sun tabbata ina masa fatan ya gyara Allah Ya fahimtar dashi gaskiya Ya bashi ikon aiki da ita. Ya bashi ikon yin adalci. Amma ba an goyi bayan wasu masu mummunan nufi ba wajen shatale shi da zubar da alkhairansa da munana zato gare shi.
NB: Wannan rubutu ba a yi shi don nuna adawa ga wata Jam’iyya ta siyasa ko goyon bayan wata ba! An yi shi ne domin fito da abinda ya bayyana ga marubucin. Idan an fassara shi da siyasa, to marubucin Dan Nigeria ne yana da Yancin yin duk Jam’iyyar da yake so (kamar yadda ake fada) kuma masu jifansa kunyi na siyasar don zargi da zagin CP WAKILI, nima ga nawa domin bashi kariya bisa abinda ya bayyana a gare ni.
Allah Ya sa mu dace.
Musa Muhammad Idris. 22/3/2019.

Leave a Reply

Your email address will not be published.