[[JAMB 2019]] Matsalolin Thumbprint

JAMB 2019/ Thumbprint 
•>Daya ga Watan April Za’ayi Jarrabawar Mock 
•> Biyu ga Watan April Za’a Fara Re-print Na Slip 
•>11th April Za’a Fara Jarrabawar JAMB. 
DANGWALA YATSA/THUMBPRINT
Tun da Farko De Hukumar ta JAMB ta bada Sanarwar Cewa Dukkan Daliban Dazasuyi Jarrabawar JAMB a Wannan Shekarar, idan sunada wani Rauni a Hannun Su ko wani Dalilin Dazaisa Na’urar Dangwala Hannun taki Daukar Hannun Su, to Sai De Suyi Rajistar JAMB Din a Babban Ofishin Su na Jamb Dake Abuja Hakama Jarrabawar Ma a Chan Zasuyi. 
Amma ga Dalibin Dayayi Rajistar JAMB din kuma Hannun sa Yakarba a Lokacin Rajistar to idan a Lokacin Jarrabawar Hannun sa be Dauka ba to Shikenan bazeyi Jarrabawar ba Sam Sam, Kamar Yanda Hukumar ta Bayyana.
Da Wannan ne Asof. Take Kara Jan Hankalin Al’umma Musamman Mata da Kada Suyi Lalle/Kunshi, har sai bayan kammala Jarrabawar. 
Haka Ma Mazan Musamman Wanda Ayyukan su suka Shafi Yin Aiki da Hannu Kamar Ayyukan Gona da Makaman tan Su Yakamata Su kiyaye Har bayan kammala Jarrabawar.
 Thumbprint ko Dangwala  Hannu Abune da Kowanne Dalibin da Yayi Rajistar ta JAMB Yayishi a Lokacin Yin Rajistar. 
Kamar Yanda Kowanne Dalibi ya Dangwala Hannun sa a Na’urar  Dangwala, Hannu Lokacin Rajistar ta JAMB Hakama Lokacin dazeyi Jarrabawar sai ya kara Dangwala Hannun sa Hakama bayan Gama Jarrabawar. 
Ka Kula Sosai da Cewa Sai ka Dangwala Hannun ka bayan kagama Dakuma kafin Fara Jarrabawar, Rashin Yin Hakan Na iya Haifar Maka da Matsala, ta absent, Wato Ace Sam Bakayi Jarrabawar JAMB din ba. 
Hukumar ta JAMB tayi Gargadin Cewa Duk Wanda Hannun sa Bekarbi Naurar Dangwala Hannun ba, to bazeyi Jarrabawar ba.
Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’a da Makarantun Gaba da Sikandiren (JAMB)
Tabayyana Ranakun 1st April Amatsayin Ranar da Za’a Yi Jarrabawar Gwaji ta Mock yayin da Tabayyana Ranar 2nd April a Matsayin Ranar da Kowanne Dalibi Zai Cire Slip Dinsa Domin Yasan Gurin Dazeyi Jarrabawar JAMB Dinsa Dakuma Rana da Lokaci ,yayin da 11 ga Watan Na April kuma Za’a Fara Jarrabawar.
Muna Fatan Allah Yabawa kowa Nasara Musamman Al’ummar ta AREWA.

Leave a Reply

Your email address will not be published.