[[JAMB 2019]] Me yasa na fadi jarrabawar JAMB???, Rubutu na 7

Meyasa Nafadi Jarrabawar JAMB? 
Kashi Na 7
( 28-03-2019)
•Shin Ban iya Computer Bane? 
•Shin Ban iya Karatun Bane? 
•Mecece Matsalar? 
Amsar Wannan Tambayar Tana Kunshe Ne a Abunda ka iya Hararowa Kai da kanka kokuma Wani wanda Yafahimci Hakikanin Matsalar ka. 
Kungiyar Asof. Tadamu Matukar Damuwa Wajen Ganin Yawan Daliban Arewa Dasuke Faduwa
 Jarrabawar JAMB,
 Dayawa Daga Cikin Su da Asof. Ta zanta Dasu wasu Sunyi Jarrabawar JAMB so Biyu wasu So Uku wani Ma da Asof. Ta Tattauna Dashi So biyar Yayi JAMB beci Ba! 
a ina Matsalar Take? 
•>Matsala Ta Goma Sha Uku
•Daina Sha’awar Jarrabawar Bayan kayi/Kinyi Rijista:-
Mafiya yawan Dalibai suna yowa rijistar wannan jarrabawar a lokacin suna son ko sha’awar yinta amma daga bisani ma’ana bayan sunyo rijistar sundawo sai su tsani jarrabawar
Dalilaine dayawa suke jawo hakan, wanda kowanne Dalibi akwai nasa dalilin dayasakashi ya tsani jarrabawar wanda wannan badaidaibane
  Matukakar kasan ko kinsan bakaratune a gabanki/gabankaba to baikamatama kayi/kiyi rijistar wannan jarrabawarba saboda koda kayi jarrabawar ba amfani zatayi makaba ma’ana bazaka taba samun nasara a abunda bakasoba.
*.* Shawarwari akan wannan matsalar:-
 1- kamar yadda nafada asama matukar kasan baka sha’awar wannan jarrabawa, to karma kayo rijista saboda, inada yakinin cewa bazaka mayarda hankali akan abinda bakasoba, wanda rashin mayarda hankalin zai iya jawo maka faduwa.
2- kada kayarda wani mutum yayi maka romon baka ma’ana yazugaka akan cewa wannan jamb dinfa ba jarrabawar arzikibace ba’acinta karka tsaya kabata lokacinka akanta. 
3- ko kai kanka idan katsaya kayi nazari zaka fahimci cewa jamb jarrabawace mai matukar amfani saboda da itane zaka iya tafiya DEGREE, batareda Ijmb, Diploma, Nce da sauransuba, saboda haka kaga maganar karka bata lokacinka akantama bata tasoba.
•>Matsala Ta Goma Sha Hudu
•Yarda Dacewa Ba’asamun Admission Da Jamb:-
Akwai wasu jama’a dasuke hurewa Daliban dazasuyi wannan jarrabawar kunne dacewa ba’asamun admission da jamb
Har saikaji suna cewa 〞ba’asamun admission da jamb nima bara nayi kuma naci 200 amma bansamu admissionba〞, 
Kada kayarda da wannan zancen domin masu yimaka irin wannan zancen suna yimaka shine domin kayiwa jarrabawar rikon sakainar kashi ma’ana kariketa lago-lago daga karshe kafadi. 
Ko kai kanka idan kaduba zakagane cewa wancan zancen nasu ba gaskiyabane, saboda zakaga cewa a garinku ko a unguwarku mutane dayawa sun sami admission da wannan jarrabawar.
•Shawarwari Akan Wannan Matsalar:-
1•Kada yawan Daliban dasukayi rijistar wannan jarrabawar yatsorataka, saboda kaji ance samada Dalibai 1.9 millionne sukayi rijista kaatsorata, ai barama samada 1.6 millionne sukayi rijista, kaga kuwa karin Dalibai Dubu Dari uku bazai hanaka samun admissionba in Allah ya yarda kaide kadage da karatu da addu’o’i
2•Kadaina yarda da jita-jita da sauran Dalibai suke yadawa cewa iyakacin 30percent daga cikin Dalibanda sukayi rijistane suke samun admission, wannan ba gaskiyabane
3• Kayarda dacewa ana samun admission da Jamb kuma kaima zaka samu in Allah yayarda
4• Daina yarda da bayanan da ba’a tabbatar da ingancinsuba. 
Mai Rubutu:- Miftahu Ahmad Panda.
(Mataimaki na musamman Ga Secretary General na Asof).
DAGA TASKAR ASOF.
Zamuci Gaba insha Allah.

Leave a Reply

Your email address will not be published.