[[JAMB 2019]] Meyasa Nafadi Jarrabawar JAMB??? Rubutu na 8

Meyasa Nafadi Jarrabawar JAMB? 
Kashi Na 8
( 01-04-2019)
•Shin Ban iya Computer Bane? 
•Shin Ban iya Karatun Bane? 
•Mecece Matsalar? 
Amsar Wannan Tambayar Tana Kunshe Ne a Abunda ka iya Hararowa Kai da kanka kokuma Wani wanda Yafahimci Hakikanin Matsalar ka. 
Kungiyar Asof. Tadamu Matukar Damuwa Wajen Ganin Yawan Daliban Arewa Dasuke Faduwa
 Jarrabawar JAMB,
 Dayawa Daga Cikin Su da Asof. Ta zanta Dasu wasu Sunyi Jarrabawar JAMB so Biyu wasu So Uku wani Ma da Asof. Ta Tattauna Dashi So biyar Yayi JAMB beci Ba! 
a ina Matsalar Take? 
•>Matsala Ta Goma Sha Biyar
•Rashin Daukar ‘Yan yatsun Dalibi(thumb print or finger print):-
Duk dacewa secretary yayi bayani, to amma wannan babbar matsalace wadda take bukatar asakeyin bayani akanta.
A shekarun baya ana samun wannan matsalar ta yatsun Dalibi suki hawa to ammafa kusani abin bai munanaba kamar bana, saboda a wadancan lokutan koda yatsun dalibi basu hau na’urar tantance dan yatsaba, to anayi masa afuwa yashiga jarrabawar a haka.
  To ammafa bana thumb print wajibine, kamar yadda hukumar jamb tafada cewa babu wani Dalibi dazaiyi jarrabawar face na’ura ta tantance ‘yan yatsunsa, wanda rashin hakan ka iya sawa a hana Dalibi ya rubuta jarrabawarsa yanaji yana gani wanda wannan bakaramar matsalabace.
 Abubuwa dayawa sukan iya zama dalilan kin daukar yatsar dalibi wadanda dolene mu nisancesu a kalla ana saura sati 1 jarrabawar, Daga cikinsu akwai:-
1- Yin kunshi(lalle), ko kumayin flower data shafi cikin ‘yan yatsu ga mata
2- Aiki da bakin man daya mutu, ma’ana wanda yayi baki ga Bakanikai
3- Yankewa da wuka ko reza a tafin hannu ko dan yatsa
4-Yin amfani da kayayyakin ayyukan gona masu bata hannu misali:- Yankan lawashin Albasa, Yagar bawon kargo, shafa ko taba ruwan bini da zugu, dadai sauransu
5- kurjewa akan ‘yan yatsu ko kuma tafin hannu.
Shawarwari Akan Wannan Matsalar
1- wajibine ga kowanne Dalibi yakiyayi aikata dukkanin wani abu dakan iya jawo masa rauni a tafin hannunsa.
2- Yanada kyau Dalibi yarage yin aikin a lokacin daya rage saura ‘yan kwanaki a fara wannan jarrabawar, saboda mafi yawan ayyukan gona suna bata hannu
3- To kamar yadda muka fada akan ayyukan gona to harda ayyukan bakanikancima suma suna bata hannu
 4- Akiyayi yawan yanke-yanke da wuka ko reza wanda idan kana/kina yawanyi tsautsayi zai iya sawa ka/ki yanke hannunki/hannunka
5- Bawai muna nufin idan anbaka aiki kakiyiba, a’a, saidai kakyautata aikin naka, ma’ana kayishi cikin nutsuwa yadda bazai cutarda ‘yan yatsunkaba.
•>Matsala Ta Goma Sha Shida
•Yarda Dacewa Bazanci Jarrabawarba:-
Dalibanmu na Arewa da dama sunada wannan matsalar
A yanzu hakan idan zakayi shira da Dalibai guda goma to shida daga cikinsu zasucemaka basa saran zasuci. 
Wannan bakaramar matsalabace domin kuwa dukkan abinda kayi imani dashi ma’ana kayarda dashi to shi zaikasance(zai faru) dakai. 
To kaga matukar kadinga hangowa faduwa aranka to kuwa babu makawa faduwar zakayi, bansan meyasaba, amman yanada kyau Dalibi yatuna cewa suma wadanda sukaci din ko kuma zasuci mutanene kamarsa, kuma Dalibaine kamarsa, watakilma yafisu kokari, amma yatsaya yana amfani da kwakwalwarsa fagen kawowa kansa faduwa, wanda wannan kwata-kwata badaidaibane.
•Shawarwari Akan Wannan Matsalar:-
1•Yana Da kyau Dalibi Yasani cewa suma Daliban dasukaci ko zasuci din mutanene kamarsa don haka, shima idan yasaka aransa cewa zaici kuma yadage da karatu da addu’o’i to zaiyi nasara dayardar Allah
2•Yana da Kyau Dalibi Yasani cewar jamb fa jarrabawace kamar kowacce jarrabawa, don haka salo dayazaibi fagen shirya musu
3• Yakamata katsaya kayi tunanin cewa jamb fa saura kiris dame-dame kashirya mata
4• Katabbatar dacewa hanyar dazakabi dai fagen cin jarrabawar maikyauce, ba mummunar hanyaba.
DAGA TASKAR ASOF.
Mai Rubutu:- Miftahu Ahmad Panda.
Zamuci Gaba insha Allah.

Leave a Reply

Your email address will not be published.