[[KA KARANTA]] MAS’ALOLI GUDA 11 NA WATAN SHA’ABAN. 01

WATAN SHA’ABAN
*_MAS’ALOLI GUDA 11 NA WATAN SHA’ABAN_*
1-Mas’ala ta farko
*”Dalilin kiran watan Sha’aban da suna SHA’ABAN”*
Malamai sunyi Ijtihadi wajan gano dalilin kiran watan Sha’aban da Sunan Sha’aban,sunyi maganganu masu yawa,amma maganar da tafi shahara da amsuwa awajan Malamai shine abinda Ibn Hajar ya fada acikin Fathul bary-:
*”An kira watan Sha’aban ne da wannan suna saboda watane da yake basu damar fita jihadi bayan Rajab ya wuce saboda shi watan Rajab watane mai alfarma da ba a yaki acikinsa,sannan watane da suke fita neman ruwa saboda zuwan watan Ramadhana,saboda a watan Ramadhana ana tsanin rana da zafi”*
@ﻓﺘﺢ ﺍﻟﺒﺎﺭﻱ ‏( 4/213 ).
2-Mas’ala ta Biyu-2
*”Falalar watan Sha’aban”*
Watan Sha’aban yana da falalar mai yawa da suka tabbata daga baki Manzon Allah ﷺ ga kadan daga cikin su;-
*i-ANA DAUKAKA AIYUKAN BAYI ZUWA GA ALLAH A WANNAN WATA*
Daga Usamatu dan Zaid R.A yace:
Nace Ya Manzon Allah,naga baka yawaita azumi awani wata kamar yadda kake yawaitawa awatan Sha’aban?? Sai yace:
*(Wannan wata wani watane da mutane suke gafala tsakanin Rajab da Ramadan,kuma watane da ake daukaka aiyukan bayi zuwa ga Allah,sai nake son nima a daukaka aiyukana ina mai azumi)*
@ﺣﺴﻨﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ
*ii-YAWAITA AZUMI ACIKINSA*
Nana A’isha R.A tana cewa:
*”Manzon Allah ﷺ baya yawaita azumin nafila mai yawa kamar yadda yake yi awatan Sha’aban,yana azumtar kusan duka watan”*.
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ.
A Hadisin Usamatu Bn zai Manzon Allah ﷺ yana yawaita azumin nafila awatan sha’aban dan a daukaka aiyukansa yana mai azumi.
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﻨﺴﺎﺋﻲ.
Daga Anas dan Malik R.A yana cewa:
*”Manzon Allah ya kasance yana yawaita azumi har muce kamar Manzon Allah baya hutawa,wani lokacin sai ya huta har muce Manzon Allah baya azumi a wannan shekarar,kuma mafi soyuwar azumi awajansa,shine azumin watan Sha’aban”&
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺃﺣﻤﺪ.
Nana A’isha R.A tana cewa:
“Manzon Allah ﷺ ya kasance yana yawaita azumin nafila har sai muna cewa baya hutawa kullum azumi yake,haka kuma yakan bar yin azumin nafila har sai muna cewa baya azumin nafila,banga Manzon Allah ﷺ ba yana yawaita azumin nafila ba kamar yadda yake yawaitawa a watan Sha’aban”
@ﻓﻲ ﺍﻟﺼﺤﻴﺤﻴﻦ ﻭﻏﻴﺮﻫﻤﺎ ﻣﻦ ﺣﺪﻳﺚ ﻋﺎﺋﺸﺔ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ.
Ummuna Salama R.A tana cewa:
“Ban taba ganin Manzon Allah ﷺ yana azumintar watanni biyu ba ajere inabanda watan Sha’aban da Ramadhana ba”
Imam Ibn Mubarak Allah yayi masa Rahama yana cewa:
“Abinda take nufi yana yawaita azumi awatan bawai yana azumtar duka watan Sha’aban ba,kuma wannan abune sananne a harshen larabci akace duka amma ana nufin mafi rinjaye”
Ibn Hajar Allah yayi masa Rahama yana cewa:
“Azumin nafilar Manzon Allah ﷺ a watan Sha’aban yafi yawa fiye da dukka sauran watanni,saboda girma da falalar wannan watan na sha’aban”.
*iii-SAMUN GAFARAR ZUNUBAI ACIKIN DAREN*
Manzon Allah ﷺ yana cewa:
*(Lallai Allah Madaukakin Sarki yana yin duba ga bayinsa a daren rashin Sha’aban sai yayi gafara ga dukkan halittunsa in banda masu yi masa shirka da masu hada wani da shi acikin bauta ko wadan da suke gaba da junansu)*
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﺑﻦ ﻣﺎﺟﻪ ﻭﺣﺴﻨﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ .
     Allah ne mafi sani
*Mu hadu a darasi na gaba insha Allah*.

Leave a Reply

Your email address will not be published.