[[KARANTA]] NASIHOHI GUDA 40 GA MATA IYAYEN AL’UMMA.

SAƘO ZUWA GA MATA IYAYEN AL’UMMA 
*_NASIHOHI GUDA 40 GA MATA_*
     Darasi na farko-(1)
*1-Zaman mace a gidanta yafi alkhairi ga fitarta ko da zuwa masallacine*.
Daga Ibn Umar Allah ya kara masa Yarda yace;Manzon Allah s.a.w yace:
*(Kada ku hana mata bayin Allah zuwa masallaci idan sun nemi izinin zuwa, amma su zauna a dakunansu shine mafi alkhairi a garesu)*.
@ﺻﺤﻴﺢ ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ ﻭﺍﺑﻦ ﺧﺰﻳﻤﺔ .
*2-Idan zaki fita ki nemi izinin mijinki,ku kuma maza ku basu izin fita idan wata buqata tasu idan ta kama*.
Daga Nana Aisha R.A yana cewa:
_”Nakancewa Annabi s.a.w kabani izini dan na fita naje wajan mahaifana”_.
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ‏( 4141 ‏) ﻭﻣﺴﻠﻢ ‏( 2770 ‏) .
Imam Iraqi yake cewa wanna Hadisin Hujjane da kuma dalili akan kada mace ta fita daga gidan mijinta koda zuwa gidan mahaifantane sai da izinin mijinta.
@ﻃﺮﺡ ﺍﻟﺘﺜﺮﻳﺐ ” ‏( 8/58 ‏)
Daga Nana Aisha R.A daga Annabi s.a.w ya ce:
(Hakika an bada izinin mata su fita idan wani buqata ta kama).
@ﻣﺘﻔﻖ ﻋﻠﻴﻪ .
*3-Yawan fitar mata da yawan yawansu yana kawo fasadi*.
Daga Abdullahi Bn Mas’ud R.A daga Annabi s.a.w yace:
*(Lallai mace al’aurace idan tafita Shaidhan yana kara kawata halittarta mafi abinda yafi samun matsayinta a wajan fuskar Ubangijinta ta zauna agidanta)*.
@ﺻﺤﻴﺢ ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ، ﻭﺍﺑﻦ ﺧﺰﻳﻤﺔ ﻭﺍﺑﻦ ﺣﺒﺎﻥ .
Shaidhan yana kara kawata adonta da kwalliyarta da kyawunta da halittarta ga maza sai su riqa tallonta har suyi sha’awarta daga nan sai sabon Allah ya biyo baya.
*4-Kada mace ta fita daga gidan mijinta sai da izininsa kuma idan bai bata iziniba to kada ta fita ta zauna agidanta shine mafi alkhairi*.
Daga Ibn Abbas R.A yace”wata mata tazo wajan Annabi s.a. w sai tace;Yaa Manzon Allah s.a.w minene miji akan matarsa?? Sai yace;
*(Kada tafita daga gidansa sai da izininsa,idan kuma ta fita tsinuwar mala’ikun sama da mala’ikun rahama tana tabbata agareta har sai ta dawo)*.
@ﺍﻟﻤﻨﺬﺭﻱ ﻓﻲ ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ ﻭﺍﻟﺘﺮﻫﻴﺐ ﻭﻋﺰﺍﻩ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﻄﺒﺮﺍﻧﻲ 
Daga Ibn Umar R.A yace:
Wata mata ga Sayyadina Umar R.A ta kasance tana zuwa Sallar Assuba da Isha’i a masallaci, sai akace mata miyasa kike fita bayan umar baya son hakan saboda kishinsa?sai tace mi ya hanashi ya hanani? Sai akace mata saboda fadan Annabi s.a.w;
*(Kada ku hana mata bayin Allah zuwa Masallatan Allah)*.
@ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ .
*5-Kata mace ta sanya turare ko kayan mashi lokacin fitarta daga gida koda zuwa masallacine*.
Daga Abi Musa Al’ash’ary R.A yace: Manzon Allah s.a.w yace:
*(Idan mace ta sanya Turare ta wuce wajan mutane dan suji kamshin wannan turare,tana da kaza da kaza)ya fadi maganganu masu nauyi sosai akanta.
Awata riwayar yace:
*(Ita mazinaciyace)*.
@ﺣﺴﻦ ﺻﺤﻴﺢ ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ ﻭﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ﻭﺍﻟﻨﺴﺎﺋﻲ.
*Turare kala biyune na mata*:
_1-Akwai turare wanda kamshinsa yake tashi daga nesa wannan haramunne mace tasanya shi ta fita sai dai ta sanya agidanta da mijinta. Domin babu abinda yake saurin tunawa namiji son jima’i irin turaran mace da kamshenta_.
_2-Marar tashin kashi sai a zo kusa da ita za’aji kamshinsa,to wannan shine ake so mace ta sanya lokacin fita domin sanya turare ibadane_.
      Allah ne mafi sani.
Mu hadu a darasi na gaba insha Allah.

Leave a Reply

Your email address will not be published.