[[KA KARANTA]] KIYAYE HARSHE

*_KIYAYE HARSHE_*
Harshe wata tsokace mai muhimmanci ajikin dan Adam,bayan zuciya babu abinda ya kai harshe amfani da hadari a jikin dan adam.
_Harshe ni’imace da Allah yayiwa dan Adam,amma idan dan Adam yayi  sakaci wajan kulawa da shi da amfani da shi yanda shari’a ta aminci sai ya kai mutum zuwa ga halaka_.
Da harshen dan adam yake ambaton Allah ya zikiri da karatun alquranin da salati ga Manzon Allah SAW,da harshene mutum yake yabon Allah ya rokesa da sunayensa da siffoninsa,sannan da harshene mutum yake fadar kalmar da take janyo masa yardar Allah da rahamarsa har Allah yayi masa gafara ya sanya shi a aljanna sanadiyyar fadar wata kalma da harshensa.
_Da harshene kuma mutum zai fadi kalmar da zata janyo masa fishin Allah da azabar Allah har ta dauwamar da shi acikin wutar jahannama har abada_.
Manzon Allah SAW yayi Umarni akan kiyaye harshe kamar yanda ya fadawa Babban Sahabinsa Mu’az bn Jabal R.A yace masa;
*(……….Ka kiyaye wannan tsoka)*sai ya kama harshensa.sai Mu’az yace;
“Yanzu ya Manzon Allah ashe za’a kamamu da laifi akan abinda harshenmu yake furtawa,?”sai Manzon Allah SAW yace masa;
*(Mahaifiyarka tayi Asararka,shin akwai abinda yake kai dan Adam acikin wuta akan fuskarsu inbanda abinda da harshensu yake furtawa ba)*
@رواه الترمذي وقال؛حديث حسن صحيح.
¤Kiyaye harshe yana kai mutum zuwa ga aljanna¤
Manzon Allah SAW yana cewa;
*(Wa zai kiyaye min abinda yake tsakanin gemunsa{wato harshensa}da abinda yake tsakanin cinyoyinsa{wato al’aurarsa}ni kuma zai tsaye masa shiga aljanna)*
@صحيح البخاري رقم-(6474)
¤Wanda ya kiyaye sharrin harshensa zai shiga aljanna¤
Manzon Allah SAW yana cewa;
*(Dukkan wanda Allah yayi masa karkuwa daga sharrin harshensa da sharrin al’aurarsa,zai shiga aljanna)*
@حسنه الألباني في صحيح الترغيب رقم:(2413)
A wata riwayar;
*(Dukkan wanda ya kiyaye harshensa da al’aurarsa,ya shiga aljanna)*
@حسنه الألباني في صحيح الترغيب رقم:(2860)
¤Harshe yana daya daga cikin abubuwan da suke saurin kai mutum gida wuta¤
Kuma an Tambayi Manzon Allah SAW akan mafi yawan abinda yake shigar da mutane aljanna sai yace;
*(Kiyaye dokokin Allah da kyawawan haleye)*.
Da aka tambayi mafi yawan abinda yake kai mutane wuta sai yace;
*(Harshe da al’aura)*
@حسن الألباني إسناده في صحيح الترمذي-رقم:(2004)
Dolene sai dan Adam ya tashi yayi yaki da harshensa sannan zai sami damar mallakarsa.
الإمام ابن القيم رحمه الله;
Yana cewa;
“Dan haka yin hakuri akan barin sabon harshe yana cikin mafi girman nau’in hakuri,domin sabon harshe yana saurin halaka dan Adam,kamar gulma da yi da mutane da zagi da giba da karya da qazafi……..dukkan wanda ya auka cikin wadan nan laifukana na harshe zasuyi saurin halakasa dan haka dole sai dan Adam ya tashi yayi hakuri ya yaki wadannan cutuka na harshensa…..”
@عدة الصابرين : (126-127)
    Allah ne mafi sani
Allah ka bamu ikon kiyaye harshenmu baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.