[[JAMB 2019]] Meyasa Nafadi Jarrabawar JAMB??? Rubutu na 9.

Meyasa Nafadi Jarrabawar JAMB? 
Kashi Na 9
( 07-04-2019)
•Shin Ban iya Computer Bane? 
•Shin Ban iya Karatun Bane? 
•Mecece Matsalar? 
Amsar Wannan Tambayar Tana Kunshe Ne a Abunda ka iya Hararowa Kai da kanka kokuma Wani wanda Yafahimci Hakikanin Matsalar ka. 
Kungiyar Asof. Tadamu Matukar Damuwa Wajen Ganin Yawan Daliban Arewa Dasuke Faduwa
 Jarrabawar JAMB,
 Dayawa Daga Cikin Su da Asof. Ta zanta Dasu wasu Sunyi Jarrabawar JAMB so Biyu wasu So Uku wani Ma da Asof. Ta Tattauna Dashi So biyar Yayi JAMB beci Ba! 
a ina Matsalar Take? 
•>Matsala Ta Goma Sha Bakwai
•Yarda Dacewa Yayana Ko Wani Dan Uwana Zaiyimin Komai:-
Wannan wata babbar matsalace datake damun Dalibai masu yawa, musammanma wadanda suke zaune a kauyuka ko karkara. 
Zakaga cewa Dalibi bazai’iya komaiba, saidai ace wani dan uwansa dayake birni yayi masa wanda hakan gagarumar matsalace.
  Wasu lokutan abin zaibaka mamaki daidaida reprinting din slip ma Dalibi bazaiyi dakansaba saikaji ance ai yayansa zaizo daga birni yace masa yaciro masa yataho masa dashi.
 Wannan Dalilin yana jawo matsaloli dayawa wanda zakaga Dalibi baya iyayin komai dakansa, kuma gashi jarrabawarnan dakansa zaiyi, to anan ake samun matsala saboda zaidauka jarrabawarma yayannasane zaiyi masa, saiyaje dakin jarrabawar kuma yaga abun bahaka yakeba.
Shawarwari Akan Wannan Matsalar:-
1- Wajibine gareka Dalibi yakasance kana iyayin kananun abuwawan dasuka shafi wannan jarrabawar. 
2- Yanada Kyau kasani cewa jarrabawar jambfa babu wakilci, kai zakayi jarrabawarka dakanka, don haka kadaina yaudarar kanka.
3- Sannan kasani cewa abubuwan da’akeyi maka kake ganin kamar gatane to bagatabane kuma bazaka gane hakanba sainan gaba.
•>Matsala Ta Goma Sha Takwas
•Yarda Dacewa Zan Iya Komai Dakaina:-
Mai Karatu kada kayi mamaki saboda kaga wadannan tagwayen matsalolin, kaidai kabiyomu domin muwarware maka inda gizo yake sakar 
Cewarfa kada kayarda ace komai yimaka za’ayi bayana nufin kayarda cewa zaka iya komaiba, komai kwarewarka akwai inda dole saika nemi taimako. 
Saboda haka kayarda cewa zaka iya komai dakanka shima matsalane, akwai abubuwanda bazaka iyaba dole sai antaimaka maka a harkar. 
•Shawarwari Akan Wannan Matsalar:-
1•Yana Da kyau Dalibi Yasani cewa bafa komai zai iya dakansaba wasu abubuwan dole sai antaimaka masa
2•To ammafa acikin abubuwan da zaka bukaci taimako kasani cewa banda kananun abubuwa dakuma jarrabawar ita kanta
3• Koda kayi jamb sau biyar ko fiyeda haka kasani cewa akwai abubuwanda dole sai antaimaka maka akansu 
4• Dazaran Dalibi yaga wani abinda yashige masa duhu yayi kokari yatuntubi masana akan al’amarin. 
Mai Rubutu:- Miftahu Ahmad Panda.
(Mataimaki Na Musamman Ga Secretary General).
DAGA TASKAR ASOF.
Zamuci Gaba insha Allah.

Leave a Reply

Your email address will not be published.