[[KA KARANTA]] LABARU A TAKAICE NA SAFIYAR YAU LAHADI.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ba daidai ba ne a yada cewa bai damu da kashe-kashe da sace mutane da a ke yi a jihar Zamfara da sauran sassan arewa maso yammacin Najeriya ba. Shugaban wanda ke magana ta sanarwa daga mai taimaka ma sa ta fannin labaru Garba Shehu, ya ce a kullum ya na sauraron rahotanni daga jami’an tsaro kan wannan illa da ke addabar al’umma.
*Shugaba Buhari ya nuna damuwa da yadda ‘yan bindigar ke da masu ba su bayanai ko tsegumi daga cikin jama’ar gari. Hakanan shugaban ya ce gwamnatin kowane lokaci ta na daukar duk matakan da su ka dace don kawo karshen miyagun irin.*
*Shugaban bai tsaya nan ba sai da ya nuna rashin jin dadin yadda ya ce wasu sun sanya siyasa a cikin lamarin da hakan ke nuna irin duhun kai da har yanzu ke cikin lamuran siyasar da a ke yi. Shugaban ya bukaci jama’a su taimakawa jami’an tsaro da bayanan miyagun irin don samun nasarar gamawa da su.*
*Kotun daukaka kara ta Akure a Najeriya ta wanke Sanata Ademola Adeleke daga hukuncin da babbar kotu ta yanke da ke nuna ba shi da hurumin takarar gwamnan Osun don rashin sahihiyar shaidar kammala sakandare. In za a tuna kotun karar zabe ta aiyana Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Osun da ya kai ga batun bai kammala ba tun farko, inda dan takarar APC da tsohon gwamna Rauf Aregbesola ya tsayar ya lashe zaben.*
*Tuni dai APC a Osun ta daukaka kara da hakan ke nuna shari’ar ka iya kai wa ga kotun koli. Ga batun kammala makaranta, kotun daukaka kara ta Akure ta yi watsi da hukuncin babbar kotun taraiya ta Bwari a Abuja da ta ce Adeleke bai kammala karatu ba. Kazalika kotun ta ce wanda ya shigar da karar Awosiyan Kinsley ba shi da hurumin yin hakan kuma an ma wuce kwana 14 daga kammala zabe wajen shigar da`karar.*
*Majalisar Mai Alfarma Sarkin Musulmin Naijeriya, ta ayyana yau Lahadi 7 ga watan 4-2019, a matsayin 01 ga watan Sha’aban 1440.*
*Jami’an gwamnatin Amurka 3 sun shaidawa kamfanin dillancin labaru na REUTERS cewa Amurka na shirin aiyana rundunar sojoji ta tsaron cikin gidan Iran a matsayin rundunar ‘yan ta’adda. Wannan shi ne karo na farko da a ke samun wannan yanayi na aiyana rundunar wata kasa a matsayin ta ‘yan ta’adda.*
*A na sa ran Amurka za ta fito da wannan matsaya karara ranar litinin. Cibiyar tsaron Amurka PENTAGON ba ta yi karin haske kan batun ba ta na mai bukatar a tuntubi ma’aikakar waje.*
*A yanzu haka dai majalisar dinkin duniya na nuna za ta ci gaba da shirin taron kasa na Libya don shirya babban zabe a kan lokaci duk da yadda dakarun da ba sa ga maciji da gwamnatin kasar na tunkarar kwace babban birnin kasar Durabulus.*
*Kwamandan ‘yan awaren da ke da tushe a birnin Benghazi da ke gabashin kasar Khalifa Haftar ya ce dakarun sa sun kutsa kudancin Durabulus inda har sun mamaye tsohon babban filkin aukar jirage na kasar.*
*Majalisar dinkin duniya da ke mara baya ga gwamnatin Durabulus ta gargadi Haftar da cewa duniya za ta dau mataki a kan sa in bai janye daga neman kifar da gwamnati ba. Tun kifar da gwamnatin Moammar Ghaddafi da yi ma sa kisan gilla da taimakon kasashen yammacin duniya a 2011, kasar Libya ta auka rudani da rashin tabbas.*
*Ibrahim Baba Suleiman*
*Jibwis Social Media*                                                                         *01-Sha’aban-1440*
*07-April-2019*

Leave a Reply

Your email address will not be published.