Anyiwa Dalibai ta’addanci a Kwalejin Horas da Malamai ta Jihar, Yobe UMAR SULEIMAN COLLEGE OF EDUCATION GASHUA

Anyiwa Dalibai ta’addanci  a Kwalejin Horas da Malamai ta Jihar, Yobe 
UMAR SULEIMAN COLLEGE OF EDUCATION GASHUA
ASOF. Ta Kadu Matuqa da Wakilanta Suka Sanar da ita Cewa, a Daren Jiya Wasu da Ake Zargin Fulani ne Sun Kai Farmaki kan Daliban a Mazaunin Su Na Gefen Makarantar Wanda Akafi Sani da Zango, inda Sukaji Wa Dalibai Guda Biyu Mummunan Rauni da Wuqa, 
Jim Kadan Bayan Faruwar Lamarin Daliban Makarantar Suka Fara Shirin Gudanar da Zangar-zangar  Lumana, kafin Daga bisani Hukumar Makarantar, ta Tabbatar da Aukuwar Lamarin, Tare da Rufe Makarantar, Kan Abunda Yafaru, Ankafe Takaddar Cewa nan da Awanni biyu Daliban Su koma Gidajen Su, Takaddar me Dauke da sa Hannun Shugaban Makarantar Dr. Muhammad Gishiwa. 
ASOF. Tana Rokon Shugabannin Makarantar, Musamman provost Dr. Gishiwa, da kuma Sarkin Garin Dasu Dauki Mataki Akan Al’amarin, tare da hukunta wanda Suka Aikata Lefin. 
Binciken ASOF. Yagano Cewar karancin Dakunan kwanan Dalibai a Cikin Makarantar ne Yasanya Dalibai Neman Dakin kwana Na Haya a kauyen Na Zango wanda Yake Kusa da Makarantar, Sannan Asof Tagano cewar ba Wannan ne Karon Farko da Daliban Suke Zargin Fulanin Wajen dayi Musu Barazana ba, Musamman idan dare Yayi Ana tare Su Akwace Musu Wayoyin Su. 
a karshe ASOF Ta Bukaci Daliban Da Su Mutunta Umarnin Shugaban Makarantar, Har Zuwa Lokacin Daza’a dauki Matakin Hana Faruwar Hakan Anan Gaba. 
Muna Jajantawa tare da Fatan Allah Yakiyaye.

Leave a Reply

Your email address will not be published.