[[JAMB 2019]] Meyasa Nafadi Jarrabawar JAMB? Rubutu na 10

Meyasa Nafadi Jarrabawar JAMB? 
Kashi Na 10(Na Karshe)
( 09-04-2019)
•Shin Ban iya Computer Bane? 
•Shin Ban iya Karatun Bane? 
•Mecece Matsalar? 
Amsar Wannan Tambayar Tana Kunshe Ne a Abunda ka iya Hararowa Kai da kanka kokuma Wani wanda Yafahimci Hakikanin Matsalar ka. 
Kungiyar Asof. Tadamu Matukar Damuwa Wajen Ganin Yawan Daliban Arewa Dasuke Faduwa
 Jarrabawar JAMB,
 Dayawa Daga Cikin Su da Asof. Ta zanta Dasu wasu Sunyi Jarrabawar JAMB so Biyu wasu So Uku wani Ma da Asof. Ta Tattauna Dashi So biyar Yayi JAMB beci Ba! 
a ina Matsalar Take? 
•>Matsala Ta Goma Sha Tara
•Addu’o’in Sharri Daga Jama’ar Gari:-
Duk Addinan Duniya babu addinin dabai yarda da addu’aba, saboda haka yinta a hanyar sharri babban hadarine
A lokuta dayawa wasu daga cikinDalibai suna fama da wannan matsalar ta addu’ar sharri daga bakin wasu abokan mu’amularsu ko kuma wasu jama’ar gari.
  Wannan kuwa yana faruwane sakamakon rashin kyautata mu’amula da mutane, kokuma hassadar jama’ar dayake cikinsu
 Wannan matsalace maihadarin gaske domin kuwa a wasu lokutan bazaka iya gane wanda yakeyi maka wannan addu’arba duk dogon tunanin dazakayi kuwa, sannan akwai mutanen da sunayin addu’a Allah zai amsa to kaga Addu’arsu gareka tanada matukar hadari.
Shawarwari Akan Wannan Matsalar:-
1- Wajibine gareka ka kyautata mu’amalarka da mutane, kodan kaci jarrabawarkama, saboda bakasan irin bakinsuba.
2- Kadage Dayin Addu’o’in neman tsari bayan ka kyautata mu’amalarka da mutane, saboda akwai makiyanka wadanda duk biyayyar dazakayi musu bazasu ganiba, saboda haka bazasu daina yimaka addu’ar rashin nasaraba
3- Yanada kyau Dalibi yadage da sadaka itama tana karya sihiri dakuma addu’o’in sharri
4- Biyayya ga iyayema tana taka muhimmiyar rawa fagen samun nasara domin kuwa da mahaifanka sun sakamaka albarka to addu’ar wani ta sharri ko sihiri bazasu bikaba. 
•>Matsala Ta Ashirin(Ta Karshe)
•Rashin Mu’amula da Asof ko kuma Wasu Kungiyoyin na Dalibai:-
Akace wai so sone amma son kai yafi, to anan dinma haka abin yake, saboda haka shiyasa nabada misali da kungiyarmu
Wannan wata matsalace datake jawowa dalibai, matsaloli dayawa, saboda koda programs dinda mukeyi a ASOF kaduba zakaga cewa sunada matukar amfani ga Dalibai saboda haka rashin sanin wadannan abubuwan yakan iya jawowa Dalibi matsala. 
Yanzu Misali Idan Mukayi Duba da wadannan matsalolin guda ashirin damuka lissafa, zaka cewa sunada matukar amfani ga Dalibai kuma rashin saninsu yakan iya jawo musu matsala. 
•Shawarwari Akan Wannan Matsalar:-
1•Yana Da kyau Dalibi Yashiga kungiyoyin Dalibai kamar irinsu Asof
2•Yana da Kyau Dalibi koda baishiga kungiyaba yakasance yana karanta programs din datakeyi 
3• Kada kayarda dacewa bazaka iya shiga ko bada gudun mawa akan kungiyoyin Dalibaiba
4• Idan har Dalibi yanason shiga kungiyar Asof to yatuntubemu. 
ALHAMDULILLAH ANAN MUKA KAWO KARSHEN WANNAN PROGRAM DIN MAI TAKEN *MEYASA NAFADI JARRABAWAR JAMB?* MUNA FATAN YA AMFANEKU.
*ZAMU BUDE GROUP DOMIN SAURARON RA’AYOYINKU AKAN WANNAN PROGRAM DIN*
    MUNGODE
Mai Rubutu:- Miftahu Ahmad Panda.
(Mataimaki Na Musamman Ga Secretary General Na Asof).
*DAGA TASKAR ASOF*
Muhadu A Wani Pogram Din Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published.