[[KA KARANTA]] FUSHI

FUSHI
.
Fushi sifface daga cikin siffar Dan Adam wadda Allah ya halicci dan Adam akan sa,kuma yayi masa umarnin yayi kokarin rage fushi ko nisantarsa abisa harshen Annabi (S.A.W).
.
Wasu masana yanayin Dan Adam suna cewa: “Fushi wani zafi ne yake faruwa acikin zuciyar dan Adam sai ya dumama jini da zuciya take har bawa sai hakan ya canja dukkan yanayi dan Adam, wasu kuma suna cewa Shaidan ne yake rura wata wuta mai zafi azuciyar dan Adam sai hakan ya canja yanayinsa. shi yasa Annabi (S.A.W) yayi umarni ga mai fushi ya nemi tsarin Allah daga shaidhan”.
.
Fushi kala biyu ne akwai:
.
1-Fushi abin yabo. Wato fushi na wajibi “Shi ne fushi don an taba Addinin Allah ko an taba wata martaba ko koyarwa ta Allah da
Manzonsa, wannan shi ne fushin da Annabi (S.A.W) yake idan an taba addinin Allah. Nana A’isha R.A tana cewa: “Da daya Annabi (S.A.W) bai taba yin fushi ba ko daukar fansa ba don an taba wani abu nasa ba sai dai yana yana fushi idan an taba Addinin Allah” (Bukhari).
.
2-Fushi abin zargi. Wato fushin da yin sa yakan zama haramun ko makaruhe. “Shine yin fushi don an taba matsayinka ko martabarka ko wani daga cikin kusa da kai, wato ana yin fushi ne don kare martabar kai ba kare addinin Allah da Manzonsa ba”.
.
FALALAR NISANTAR FUSHI DON AN TABA KA KO AN BATA MAKA RAI.
.
1-Barin fushi yana jawowa mutum samun son Allah a gare shi. Allah yana cewa: ”Waɗanda suke ciyarwa a cikin sauƙi da tsanani kuma suke masu haɗiyewar fushi, kuma masu yafe wa mutane laifi. Kuma Allah
Yana son masu kyautatawa” (Suratu Al’imran Aya ta 134).
2-Nisantar fushi da barinsa wasiyyaace daga cikin wasiyyoyin Manzon Allah (S.A.W). Wani mutum ya cewa Manzon Allah (S.A.W) kayi min wasiyya sai yace:
(Kada ka yi fushi) Sai ya sake maimaitawa kayi mini wasiyya sai yace: ”Kada kayi fushi” (Bukhari).
.
3-Wani mutum ya cewa Annabi (S.A.W) ka bani labari da wadansu kalmomi wanda zan rayu akansu amma kada ka yawaita min su, sai yace da shi: ”Ka nisanci fushi” sai ya kara tambayarsa akan haka sai yace: ”Ka nisanci fushi” (Silsilatus Sahiha 884).
.
4-Ka nisanci fushi za ka shiga Aljanna. Wani mutum ya cewa Manzon Allah (S.A.W) kayi min nuni zuwa ga wani aiki da zai shigar da ni Aljanna sai yace: ”Kada ka yi fushi zaka shiga Aljanna”.
.
5-Ka nisanci fushi kana da ‘yan matan Hurul’in. Manzon Allah (S.A.W) Yana cewa: ”Dukkan wanda ya hadiye fushi alhalin yana da damar daukar fansa, Allah madaukakin Sarki zai kira shi a gobe Alqiyama a tsakiyar mutane ya bashi damar ya zabi ‘yan matan Hurul’in yadda yaga dama).
.
Amma yin fushi don Allah saboda an taba Addinin Allah ko martabar Allah da Manzonsa (S.A.W) wannan fushi wajibi ne. Saboda Hadisin Nana A’isha (R.A) tana cewa: Annabi (S.A.W) bai taba yin fushi ba ko daukar fansa ba ko sau daya ba sai idan an taba Alfarmar Allah” (Bukhari da Muslim)
.
Allah Ya amfanar da mu baki daya Ya kuma bamu ikon hadiye fushinmu, ameen.

Leave a Reply

Your email address will not be published.