[[KA KARANTA]] MENENE GOOGLE ADS???

MENENE GOOGLE ADS???
Wannan shine tambayar da mutane suke ta maimaitawa a karkashin rubutuna da nayi akan cewa “whatsapp zasu sanya ads”.

A takaice Google ads na nufin dandamali ne dake baiwa mutane damar tallata hajar su, su zasu baiwa google wannan tallan, shi google sai ya tallata musu bayan sun biya wannan google din kudin.

Sannan shi wannan ads din ya hada da hoto, hoto mai motsi da sauransu.

Ba lallai bane wanda baya harkar kirkirar shafi (website ko blog) don samun kudi ko sanya video a YouTube don samun kudi ya fahimci wannan bayani da nayi.

Wadanda basu wancan harkar na sama, ga bayanin yadda zaku fahimci menene ads koko yadda zaku gane shi.

Bari mu fara da YouTube, a lokacinda ka shiga YouTube zaka bude wani video, da zaran ka bude zakaga wani takaitaccen video wanda tsawon shi bai kai minti daya ba ya fara playing, a gefen damar wannan video zakaga skip ad koko ka skipping koko ka barshi ya kammala kafin asalin video da kake buqata ya fara playing. Wannan takaitaccen video shine ads na YouTube, duk YouTube channel da kaga yanada wannan ads din to kudi yake samu dashi.

Na biyu shine shafi wato website ko blog ko wasun su.
Idan ka shiga website wani lokaci zakaga wasu hotuna a shafin wanda suke buqata a latsa su, da zaran ka latsa zasu kaika wani wuri, sannan zakaga suna da wani alama a saman su ta hannun dama kamar $. Su wadannan asalin ba hoto na zahiri bane domin suna tattare da liqau (link) a tattare dasu. Wannan sune misalan ads na shafi (website) domin ganin misali zaka iya shiga shafi na domin kara fahimtar bayani na www.arewagist.com.ng

Na uku shine na masu kirkirar application, application kamar su keyboard, true caller, TouchPal, facebook, WhatsApp, games da sauransu, amma su masu application sunan nasu AdMob ne.

Yadda zaka gane application yana da ads shine, idan ka bude application din zakaga wasu hotuna suna bullowa suna buqatar a latsa su, wasu ma suna motsi, wanda yake amfani da True caller zai shaida hakan. Wasu application suna dashi, wasu basu dashi, kamar facebook bayida ads haka ma WhatsApp, shine yanzu WhatsApp suke so su sa a nasu saboda yanzu haka sunada masu mu’amala dasu sama da biliyan daya.

Wani lokacin saboda jahilcin mutum, idan yaga irin wadannan ads din a cikin application na wayar shi sai yace virus ya kama wayar shi, Malam ba virus bane, wanda ya kirkiri app din shine yasa don ya samu kudi.

Wannan takaitaccen bayani akan ads kenan, please duk wanda bai fahimci wani abu ba zai iya tambaya ta anan kasa ko ta message.

Daga dan uwanku
Abu Abdirrahman Kaltungo
20th April, 2019

Leave a Reply

Your email address will not be published.