Me Yakamata Nayi Bayan Nayi Jarrabawar JAMB? Kashi na 01

Abunda Yakamata Mu Sani Bayan Rubuta JAMB

Kashi Na 1 (Cigaba)

(25-04-2019)

Daga Taskar ASOF.

•>Me  Yakamata Nayi Bayan Nayi Jarrabawar JAMB?

•>Me Yayi Saura?

•>Shin Najira Kawai Za’a Ban Admission?

Wani Lokacin Zumudin da Dalibi Yakeyi Na Rubuta JAMB Dinsa yana karewa ne da Zaran Sakamakon JAMB Yafito, ta Yuwu be Ci Makin din Dayake So Yaci ba,

Shin Me Yakamata Nayi?

•Wannan Tambayar Tana da Muhimman Ci Sosai.

Bayan Fitowar Sakamakon JAMB din ka Abubuwa Nafarko Dazaka Fara Dubawa Sune:

1•Makin Nawa kasamu?

2•Makin Nawa Jami’ar Daka Nema Takeso ?

3•Makin Nawa Ake Nema a Departments din da Kake So?

4• Wanne Tsari Makarantar Daka Nema Takebi Wajen Bada Admission?

Idan Kuna Biye Damu a Darasin Mu Nabaya Munyi Bayani Akan Abu Biyu Daga Cikin Hudun da Muka Lissafo a Sama, zamu Dora Daga inda Muka Tsaya.

•Makin Nawa Ake Nema a Departments din da Kake So? Yana Daga Cikin Babbar Matsalar Da’ake Fuskanta, wani Lokacin Rashin Sanin Adadin Makin Din Da’ake Bukata, a Department din da Dalibi Yake Nema, Misali Kana Neman Computer Science a Federal University Dutsenma, Amman baka Sani ba ko Akwai wani Maki Na Musamman Da’aka Kebance dole Sai ka samu a Jamb Dinka kafin Abaka Admission din, wani Lokacin kuma Abun yana Komawa ne kan Combination Dinka Na SSCE idan akwai wani darasin da’ake Bukatar Dole Sai kaci.

•>Yanda Za’a Magance Wannan Matsalar:
Nafarko De Dole Dalibi Yazama yana Bibiyar Duk wasu Abubuwa Na Makarantar Dayake Nema Dakuma Department din, Sannan yana da kyau kasamu Wadan da Suke Wannan Department din Sudinga Fada Maka Abunda Yakamata Kayi, wani Lokacin kuma Sai kaje Wajen HOD din Dakan ka Domin Samun Cikakken Bayani.

•Wanne Tsari Makarantar Daka Nema Takebi Wajen Bada Admission:
a Shekarar 2017 Wani Dalibi Ya Rubuta JAMB Yasamu Adadin Makin din Da’ake Nema a Jami’ar Kimiyya da Fusaha ta Wudil Sai De Amma bayan Haka Besan wani Abu da Zeyi ba Anan Gaba, Yaje Gida Kawai yana jiran Admission bayan Lokaci Me Tsawo sai aka bukaci Zuwa Jami’ar Domin Tan-Tancewa Zuwan sa ke da Wuya Aka Tambaye Shi Slip Dinsa wanda yabiya Kudi kuma yayi online registration Amma kash!  Besani ba hakan tasa Ba’a Saurare Shi ba Yakoma gida.

Tabbas Dole ne Kasan irin Tsarin da Makarantar take bi shin Post-UTME takeyi kokuma Departmental Screening?

Da Zaran kaga Sakamakon JAMB din ka Yafito Kuma kasamu Makin din Da’ake Bukata, To daga Wannan Lokacin Zaka Fara Bibiyar Al’amuran Makarantar Sau da Kafa.

Zamu Cigaba insha Allah.

KARKU MANTA MATSALAR DALIBI DAYA MATSALAR MUCE DUKA KUZO MUHADU MU MAGANCE TA

Leave a Reply

Your email address will not be published.