[[Ka karanta]] Ya zama dole ga kowanne dalibi yayi katin Shaidar zama dan kasa.

•Ya zama dole ga kowanne dalibi yayi katin Shaidar zama dan kasa

•Yanzu yin rajistar Jamb bazai yuwu ba, dole sai da Katin zama Dan kasa (NIMC)

•Zamuyi kokarin mun kawar da Malpractice a Jarabawar Jamb

Hukumar Shirya jarabawar Share fagen shiga jami’a ta kasa (Jamb) tace “daliban da zasuyi jarabawar jamb a shekarar 2020 zasuyi rajistar jamb ne da lambar su ta katin shaidar zama Dan kasa (National Identity Management/NIM). Inda hakan yake nufin dole kowanne dalibi yayi katin na shaidar zama Dan kasa. Hukumar ta bullo da wannan hanyar ne saboda ta magance matsalar yin rajista sau biyu lokacin da akeyin rajistar jarabawar ta jamb.

Dr. Benjamin ne ya bayyana haka a wani workshop na kwana daya da hukumar NECO ta shirya a garin keffi dake jihar Nasarawan Nigeria, a ranar Juma’ar data gabata.

Mr. Benjamin din yace zasu hada gwiwa ne da hukumar ta NIMC, saboda duk wani examination malpractice yana farawa ne tun daga lokacin da akeyin registration din dan haka suka yanke shawarar yin amfani da lambar ta katin shaidar zama Dan kasa. Hakanan ya kara da cewa registration din na jamb bazai rika wuce wata daya ba (Kwana 30) kamar yadda akeyi a baya, daga nan kuma ya roki iyayen dalibai akan su daina karfafa ma yaran su gwiwa akan cin amanar Jarabawa.
Da yake jawabi akan matsalolin biometric, Mr. Benjamin yace:

Hukumar ta gama shiryawa tsaf domin kawar da wannan matsalar a wannan shekarar ta 2020. Inda yace; a shekarar 2018 mun samu matsalar biometric na dalibai daya kai kimanin dubu ashirin da hudu da dari hudu da tis’in. (24,490) amma a shekarar 2019 Ashirin da biyu (22) kawai muka samu. Ya kara da cewa babu wata CBT Center da zasu bata damar gudanar da jarabawar ta jamb sai center dinda take mallakin administrators din su.

A bangaren yin rajistar ta jamb, wasu a nasu bangaren suna ganin kakaba wannan dokar kamar wata hanya ne ta hana dalibai yin karatu, musamman mutanen karkara kamar yadda kowa ya sani cewa ba wata kulawa suke samu ba, kama tun daga gwwmnatin jiha har zuwa gwamnatin tsakiya, Dan haka suna ganin kamata yayi hukumar ta Jamb ta bullo da wata hanya amma ba wannan ba; inda wasu kuma suke ganin hakan yayi daidai sosai, saboda itane hanya daya tilo ta tsabtace ilimin Jami,a a kasar tun a matakin farko.

Leave a Reply

Your email address will not be published.