Post-UTME Alert ! • 2019/2020 Academic Session • UNIVERSITY OF MAIDUGURI

• Post-UTME Alert !

• 2019/2020 Academic Session

• UNIVERSITY OF MAIDUGURI

• 01/07/2019.

Hukumar gudanarwa ta Jami’ar tarayya dake Maiduguri a Nigeria (Unimaid) ta fitar da Institutional Cut off Point dinta.
A wata takarda da hukumar ta fitar mai dauke da sa hannun rajistara na Jami’ar Mal. Tijjani Bukar, an bayyana cewa duk dalibin da yaci maki 160 a jarabawar sa ta jamb to yanada damar da zaiyi rajistar ta Post-UTME akan kudi naira dubu biyu (N2000) matukar dai ya saka Jami’ar a zabin sa na Jamb din.
Hakazalika, Za’a fara rajistar Post-UTME din ne a yau litinin (1st June, 2019) inda za’a rufe rajistar a ranar 30th October, 2019.
Dangane kuma da masu Direct Entry, Jami’ar tana sanar dasu cewa duk Wanda yake da Second Class lower a diploma dinshi, ko kuma Point Tara (9 point) a NCE/IJMB, ko kuma Second Class lower a digiri dinshi na farko to shima zai iya yin Online Screening Exercise din Dan Neman gurbin karatu a jami’ar

Leave a Reply

Your email address will not be published.