Labaran Safiyar Talata 02/07/2019CE – 29/10/1440AH. Cikakkun labaran

Labaran Safiyar Talata 02/07/2019CE – 29/10/1440AH. Cikakkun labaran

‘Ya’yan jam’iyyar APC sun ja-kunnen Buhari game da nada masu ruwa-biyu a cikin sababbin Ministocinsa.

Shugaba Buhari, ya maye gurbin shugaban hukumar NHIS, Farfesa Usman Yusuf, da Farfesa Mohammed Sambo.

Gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi, ya ce ba kowane baqo za su rika bari yana shigowa jiharsu yana zama ba.

Ma’aikatan jihar Kogi sun bayyana rashin goyon bayansu ga Yahaya Bello.

Wata babban kotu da ke Abuja ta bayar da umarnin kamo shugaban hukumar kwallon kafa ta kasa, Amaju Pinick.

Tsohuwar Minista a Najeriya,  Amina Mohammed ta ce tana goyon bayan a bai wa ‘yan luwadi da madigo ‘yancin yin auren jinsi .

Mutane 5 sun rasa rayukansu a sanadiyyar wani hatsarin mota da ya rutsa da su a kan hanyar Bauchi zuwa Jos.

Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello ya ce jihohin Arewa kawai za a su iya bayar da duk filayen da ake bukata don aiwatar da Ruga.

An yi ikirarin cewar jiragen yakin Isra’ila sun kai hare-hare a wasu yankunan Sham dake hannun gwamnatin Bashar Al-Asad na Siriya.

AFCON: Ivory Cost ta ci Namibia 4:1 a wasan jiya.

AFCON: Morocco ta ci South Africa 1:0 a wasan jiya.

AFCON: Senegal ta ci Kenya 3:0 a wasan jiya.

Wane Labarine Yafijan Hankalinka/Ki

Leave a Reply

Your email address will not be published.