Taraba State University (TASU) Post-UTME Alert !

• Post-UTME Alert !

• Taraba State University (TASU)

• 2019/2020 Academic Session

06/07/2019

Hukumar gudanarwa ta Jami’ar Jihar Taraban dake Nigeria (TASU) tana sanar da daukacin daliban da suka saka jami’ar a zabin su na farko, da kuma wadanda suka nemi gurbin karatun ta Direct Entry (DE) da suje suyi rajistar Screening Exercise online. Daliban da suke da damar yin rajistar sune wadanda sukaci maki 160 zuwa Sama a Jamb din su.

A wata takarda da hukumar ta fitar mai dauke da sa hannun rajistara na Jami’ar Dr. Joseph M. Lucas an bayyana cewa za’a rufe yin rajistar ne a ranar 31 ga watan August (31st August, 2019)

Dan haka kowanne dalibi yayi kokarin yin rajistar kafin lokacin rufewa, Sannan dalibi zai biya kudin Screening Exercise din  Naira dubu biyu (N2000).

Leave a Reply

Your email address will not be published.