[[JAMB 2019]] Shin Jarabawar Jamb ta Shekarar 2019 an fadi ne ko an ci ?

•Shin Jarabawar Jamb ta Shekarar 2019 an fadi ne ko an ci ?

Akwai kimanin Dalibai Miliyan daya da dubu Dari takwas da tamanin da Shida, da Dari biyar da Tara (1,886,509) da sukayi rajistar jarabawar ta Jamb a kakar karatu ta Shekarar 2019. Inda kuma dalibai kimanin Miliyan daya da dubu dari takwas da Ashirin da shida, da Dari takwas da talatin da tara (1,826,839) suka samu damar yin jarabawar ta jamb, kenan akwai dalibai dubu Hamsin da Tara, da Dari shida da sittin da bakwai (59,667) da basu samu damar yin jarabawar ta Jamb ba. A yayinda kuma a Shekarar 2018 aka samu dalibai dubu talatin da bakwai da Dari biyar da goma sha shida (37,516) da basu samu damar zana Jarabawar ba. To idan mun duba zamuga wananan shekarar ta 2019 adadin yafi yawa idan aka kwatanta Dana shekarar 2018 watakila hakan baya rasa Nasaba da matsalar Thumprint da daliban wannan shekarar suka samu.
Hakanan kuma akwai masu bukata ta musamman kimanin su Dari Uku da Saba’in da Biyu (372) da sukayi rajistar ta Jamb, Inda adadin ya zarce na Shekarar 2018 yayinda aka samu masu bukatar ta musamman su Dari Uku da goma Sha biyar (315) da sukayi rajistar ta Jamb.

•Ga Kididdigar Daliban da Sukayi Jamb din a Shekarar 2019

1• 200 zuwa Sama:-
Akwai dalibai kimanin Dubu Dari hudu da Ashirin da Bakwai, da Dari daya da Hamsin da shida (427,156) da sukaci maki 200 zuwa sama.

2• 190 zuwa 199:-
Kimanin Dalibai Dubu Dari da Sittin, da dari takwas da tamanin da biyu ne (160882) sukaci maki 190 zuwa 199 a Jamb dinsu

3• 180 zuwa 189:-
Akwai dalibai dubu Dari biyu da Dari bakwai da Saba’in da tara (200779) da sukaci maki daga 180 zuwa 189

4• 170 zuwa 179:-
An samu dalibai Dubu Dari biyu da talatin da Bakwai da Dari hudu da Ashirin da Biyar (237425) da sukaci maki 170 zuwa 179

5• 160 zuwa 169:-
Kimanin Dalibai Dubu Dari biyu da Hamsin da bakwai da goma Sha bakwai (257017) da sukaci maki 160 zuwa 169

Wannan Shine Kididdigar da Hukumar ta Jamb din ta Fitar

•Madogara
STATISTICAL REPORTS on 2019  UTME APPLICATION

Leave a Reply

Your email address will not be published.