HANYOYIN GUDA 15 NA SAMU DACEWA DA ADDU’AR ANNABI SAW A GAREKI KA

HANYOYIN GUDA 15 NA SAMU DACEWA DA ADDU’AR ANNABI SAW A GAREKI KA

Idan kana son samun dacewa da addu’ar Manzon Allah ﷺ a gareka to ka lazuminci wadan nan aiyuka na alkhairi tare da ikhlasy da koyi da Annabi ﷺ acikin su, hakan zai sanya ka sami dacewa da addu’ar Manzon Allah SAW ta albarka ko ya nema maka gafara ko samun albarka agareka, ita kuma addu’ar Manzon Allah SAW karbabbiya ce awajen Allah.

Ba wai Manzon Allah ﷺ zai yi mata addu’ar bane ba yanzu, Manzon Allah SAW baya raye ya koma zuwa ca Ubangijinsa, amma Manzon Allah SAW yayi addu’a ga mai aikata wadan nan aiyuka tun yana raye, dan haka duk wanda ya raya sunnar wannan aiki to yana dacewa da wannan addu’ar ta Manzon Allah SAW, Allah ne Mafi sani.

1-AIKI NA FARKO
*Yin sallar nafila Raka’a hudu kafin sallar La’asar*
Bata cikin Nafiloli goma sha biyu na yau da kullum, wannan nafila ce ta musamman da Manzon Allah SAW ya kwadaitar akan yin ta tare da addu’a ga wanda yake yin wannan sallah, itace bayan anyi rikan sallar La’asar to mutum ya tashi ya kawo sallar nafila raka’a hudu.

Manzon Allah ﷺ yana cewa
*(Ya Allah kayi rahama da jin kai ga wanda yayi sallar nafila raka’a hudu kafin sallar La’asar)*
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ‏( 430 ‏) ﻭﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ ‏( 1271 ‏)

2-AIKI NA BIYU
*Aikin Limanci da Ladanci*
Limanci da Ladanci na sallah suna cikin mafi girman aiyuka na aikin musulinci na yau da kullum, domin suna suke hada kawunan al’ummar musulmai guri daya dan aikata aiyuka iri daya a kowane yini sau biyar.

Hakika Manzon Allah ﷺ yayi addu’ar shiriyar Allah ga Liman yayi addu’ar gafara ga Liman, sai yake cewa:
*(Liman abin larumcewa ne shi kuma Ladan abin amincewa ne, Ya Allah ka shiryar da limamai ka datar da su, ya Allah kayi gafara ga Ladanai)*
@ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ ‏( 517 ‏) ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ

LIMAN
*Ka yarda da shi duk abinda ya aikata shine abin koyi ga Allar ka ka lamirce masa lahiraka*

LADAN
*Ka amince da shi cikin lokacin sallah shine yake fada mata lokacin sallah yayi kayi salla lokacin buda baki yayi ka ajiye azumi* wadan nan ba kananan aiyuka bane ba a musulinci.

3-AIKI NA UKKU
*Yin aiki hajji*
Yin aiki hajji hanyace ta dacewa da adduar Manzon Allah SAW ga mai aikin hajji musamman aikin hajji da akayi na dha’a da koyi da Manzon Allah SAW acikinsa.

Manzon Allah SAW yana cewa:
*(Ya Allah kayi gafara da jin kai ga alhazai, kuma kayi gafara ga wanda ya nemawa alhazai gafara)*.
@ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ ﺍﻟﻜﺒﻴﺮ ‏( 1451 ‏)

4-AIKI NA HUDU
*Nemawa masu yin aikin hajji gafara* Alhazai da suke yin aikin hajji sai ka ce ya Allah ka gafartawa dukkan masu aikin hajji, hakan yana janyo maka dacewa da adduar Manzon Allah SAW ta gafara agareka.

Manzon Allah SAW yana cewa:
*(Ya Allah kayi gafara da jin kai ga alhazai, kuma kayi gafara ga wanda ya nemawa alhazai gafara)*.
@ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ ﺍﻟﻜﺒﻴﺮ ‏( 1451 ‏)

5-AIKI NA BIYAR
*Yin aski ko sausayi a lokacin da mutum ya gama aikin hajji ko Umara*

Manzon Allah ﷺ yana cewa
*(Ya Allah kayi rahama da jin kai ga wadanda sukayi aski)* sai Sahabbai suke ce:Da masu sausaye, sai yace
*(Ya Allah kayi rahama da jin kai ga wadanda sukayi aski)*sai suka ce da masu sausaye, sai yace
*(Ya Allah kayi rahama da jin kai ga wadanda sukayi aski)* sai suka ce da masu sausaye sai yace:
*(Ya Allah kayi rahama da jin kai ga wadanda sukayi sausaye)*
@ﻭﻣﺴﻠﻢ

        Allah ne Mafi sani

Mu hadu a Darasi na gaba insha Allah

Leave a Reply

Your email address will not be published.