[[Ka Karanta]] Abunda Yakamata Mu Sani Bayan Rubuta JAMB

Abunda Yakamata Mu Sani Bayan Rubuta JAMB

(AREWA STUDENTS ORIENTATION FORUM)

Kashi Na 4

(26-08-2019)

Daga Taskar ASOF.

•>Me  Yakamata Nayi Bayan Nayi Jarrabawar JAMB?

•>Me Yayi Saura?

•>Shin Najira Kawai Za’a Ban Admission?

Wani Lokacin Zumudin da Dalibi Yakeyi Na Rubuta JAMB Dinsa yana karewa ne da Zaran Sakamakon JAMB Yafito, ta Yuwu be Ci Makin din Dayake So Yaci ba.

Shin Me Yakamata Nayi?

•Wannan Tambayar Tana da Muhimman Ci Sosai.

Bayan Fitowar Sakamakon JAMB din ka Abubuwa Nafarko Dazaka Fara Dubawa Sune:

1•Makin Nawa kasamu?

2•Makin Nawa Jami’ar Daka Nema Takeso ?

3•Makin Nawa Ake Nema a Departments din da Kake So?

4• Wanne Tsari Makarantar Daka Nema Takebi Wajen Bada Admission?
********************************************
«»Mafi yawan Jami’o’i sunyi jarrabawarsu ta Post Utme, wasu kuma suna rijista,

 Ammani Jami’ar da Na nema ko Maganar fitarda Cut-off mark batayi, Shin menene mafita?

•Ni kuma Jami’ar da na nema har munyi post utme, kuma sakamakonmu har yafito, Tambayata itace: Shin Bayan Samun Nasara a Jarrabawar Post Utme menene mataki nagaba?
(WATO NEXT LEVEL)

       kadan kenan daga cikin tambayoyin da Dalibai sukeyiwa ASOF.

              Q1.

•>A Zahirin gaskiya mafi yawan makarantun Najeriya musamman ma jami’o’i suna tsaka dayin rijistar jarrabawarsu ta post-utme, wasu makarantun ma harsunyi jarrabawartasu ta post-utme, amma har a yanzu haka akwai makarantun da ko cut-off mark basu fitarba, wanda hakan yasaka irin Dalibin dasuka nemi wadancan makarantu suke zaune a cikin hali na Dar-Dar, harma wasu daga cikinsu suke tunanin cewa Anya kuwa Bana Makarantar nan zata debi Dalibai kuwa?

A zahirin gaskiya dukkanin wata Jami’a tana daukar Dalibai a kowanne Session, saboda haka babu wata shekara dazatazo tawuce wata makaranta bata debi Dalibai a wannan shekarba.

  A mafi yawan lokuta Dalilin dayake sawa asamu wannan jinkiri shine: YAKASANCE CEWAR WANNAN MAKARANTAR  BATA DADE DAFARA KARATUNTA  BA, Na KAKAR Karatu ta 2018/2019

 Ballantana tayi maganar diban wasu sababbin Daliban.

Saboda haka kasancewar makarantar daka nema a cikin sahun irin wadannan makarantun ba abune na damuwaba ba, hasalima irin wadannan makarantu suna taimakawa Dalibai sosai fagen samun admission,

 domin kuwa koda Dalibi yanemi wata makarantar baisamuba zai iya canjawa yakoma irin wadannan makarantu.
 
Saboda haka don yakasance makarantar daka nema takasance a irin wannan sahu ba abin damuwabane, matukar kanada tabbacin cewar bazata fitarda makin dayawuce wanda kasamu a jarrabawarka ta jamb ba (Kusani Babu Jami’ar Da zata Fidda Maki Qasa da 160)

 Idan kuwa yakasance kana tunanin makin da wannan makaranta zata fitar zai iya haura makin dakasamu a jarrabawartaka, to abinda yafi shine kacanja zabinka zuwa wata makarantar wacce ta fitar da makin da bai wuce wanda kasamuba.

                Q2

 Daga lokacin daya kasance Dalibi yayi jarrabawarsa ta post utme to babu wata jarrabawa kuma dazai sakeyi, saidai yakoma gida yasaurari fitowar makinsa na post utme wanda bayan fitowar wannan maki ne makarantar da yanema zatayi amfani da  maki din daya samu domin duba yiwuwar bashi admission ko akasin haka.

  A takaice dai Bayan kammala jarrabawar POST UTME  babu wani abu dayarage sai ADMISSION Saboda haka post utme itace siradin karshe.

   A karshe ASOF tana shawartar Daliban da basuyi jarrabawarsu ta post utme ba sainan gaba, dasu dage da karatu da Addu’o’i domin samun nasara, Tare Kuma da Bibiyar Al’amuran Makarantar Dasuka Nema a ko Yaushe Koda kuwa Kayi Jarrabawar.

•ASOF IS YOURS

  *Munayin Komaine Dominku Dalibai*

 Muna  maraba da tambayoyi ko shawarwarinku.

    MUNGODE

Zamu Cigaba insha Allah.

KARKU MANTA MATSALAR DALIBI DAYA MATSALAR MUCE DUKA KUZO MUHADU MU MAGANCE TA

Marubuci:- *Miftahu Ahmad Panda*
*(Mataimaki Na Musamman Ga Secretary General Of Asof)*.
ASOF. (08088119753)

Leave a Reply

Your email address will not be published.