[[KA KARANTA]] LALLAI YA DACE MUSULMI SU SAN WANNAN…

LALLAI YA DACE MUSULMI SU SAN WANNAN…

A Taqaice: Dr Zakir Abdulkareem Naik haifaffen gaarin Mumbai ne dake kasar India, kuma an haifeshi ne a ranar 18 ga watan  october, 1965.

Kwararren Likita ne (tunda a karon farko ya karanta MBBS), kafin ya shiga fage na kira zuwa ga Addinin Musulunci da qoqarin fahimtar da Musulmi asalin Addinin da Annabi Muhammad (saw) yazo dashi.

Al’amarinsa ya bayyana ne daga shekarar 1995, inda ya bayyana a matsayin wani abin ban al’ajabi ga Al’ummar Duniya, saboda tsabagen karfin hadda, iya tattaunawa da wanda ya sa6a masa a Addini ko a kan wata fahimta, tare da sanin hanyoyi da dabarun fahimtar da mai neman fahimta cikin ruwan sanyi.

A wannan karnin idan aka ‘dauke mutane irinsu Sheik Muhammad Nasirudden Al-Albany, abune mai wahala ka nemo mutum Irin Zakir Naik, wanda ya sallama lokacinsa, karfinsa, lafiyarsa, dukiyarsa don shiga mabanbanta bangarori na Duniya, Don isar da saqon Allah. Da wahala a wannan zamanin ka samu wani mutum da yayi sanadiyyar shigar da mutane (maza da mata) masu tarin yawa cikin Addinin Musulunci irinsa.

Daga cikin akhairan da yayiwa Duniyar Musulunci shine:-
1- Samar da cibiyar bincike da ya’da ilimin Addinin mai suna Islamic Research Foundation (IRF).
2. Samar da gidan TV na Peace TV, domin ya’da karantarwar Addinin Musulunci ga kasashe Daban-daban.
3. Gina Makaranta don haddatar da yara kanana Ilimi, tare da koyar dasu hanyoyin tattaunawa da mabanbanta Addinai.
4. Fara samar da ginin Jami’ar Musulunci a wasu kasashe tare da niyyar samar da ire-irensu a kasashe masu tarin yawa a Duniya.
5. Rubutu da wallafe wallafe wurin karyata zargi da kafiran Duniya da kuma ‘yan Boko Aqeedah sukeyi ga Addinin Musulunci.
6. Yakar masu bautar wanin Allah ta fuskar hujja da tattaunawa da manyan Malamansu don bayyana gaskiya ga Duniya musamman Duniyar yankinsa na India, kasar da ta shahara da bautar humaka, shanu, awaki, duwatsu, mutane da sauransu…

Wannan gagarumin aikin da matashi ‘dan shekaru  53 kacal ya keyi, ha tayarwa da Duniyar kafirai hankali, ganin cewa suna yiwa Musulunci illa ta hanyar kazafi da karairayi, amma a yau ga wani ya fito yana karyatasu da hujjoji tare da kalubalantarsu su fito suma su kare nasu Addinin.

Don haka, kusan tun a shekarar 2010, kasar UK da Canada suka hana masa shiga kasashensu, don gudun bayyanar gazawarsu da raunin Addinin Yahudu Da Nasara ta fuskar hujja.

WANNE HALI YAKE CIKI???
Matsaloli sun tsananta gareshi ne, bayan zarginsa da kasar Bangladesh tayi akan kisa da wani mutum yayi a wani cafe dake yankin Dhaka, wanda yayi sanadiyyar mutuwar Mutane kusan 22, kasar tayi zargin cewa makashin yayi kisan saboda tunzurawa Dlda kwarin gwiwa da ya samu ta hanyar sauraron karatuttukan Dr Zakir Naik. Don Haka kasar ta jukunta dakatar da gidan TV na Peace TV (wacce ke matsayin kafa da take ya’da karatuttukan Zakir Naik).

Dr Zakir Naik yayi musun wannan zargin a wata lecture da ya gabatar tare da nuna muhimmancin ran dan Adam a Addinin Musulunci, da yanda kayi gargadi ga duk wanda ya kashe wata rai.

Daga baya Wata kungiya mai Bincike a kasar India (NIA), tayi rahoto na ‘yan sanda game da cibiyar Islamic Research Foundation, tare da zargin cewa saqon da wannan cibiya ke ya’dawa yana da tasiri wurin sanya gaba da kiyayya a tsakanin mabanbanta Addinai. Wanda hakan ya bayu zuwa ga hukuncin  dakatar da cibiyar daga gudanar da ayyukanta har na tsawon shekaru biyar.

Zargin da lawyer Mubeen Soltar, wanda shine lawyer mai tsayuwa a madadin cibiyar, ya musanta haka luma ya bayyana cewa idan aka zartar da wani hukunci game da cibiyar to ba a nufi adalci ba.

Kungiyar kula da rikice-rikice na tattalin arziki a kasar India itama ta kulla zargi akan Dr Zakir Naik akan cewa cibiyar da ya samar ta IRF tana da hannun wurin salwanta ko sama da fa’di da wasu kudade, har ta hukunta toshe duk wata kafa da cibiyar ke samun tallafi.
(Kamar yanda tashar Aljazeerah ta bayyana).

To amma ga duk wanda ya san ko yake bibiyar Dr Zakir Naik, ya san cewa wannan zargin abin karyatawa ne, kuma ba gaskiya bane, saboda yanda aka shedi wannan mutum da tsantseni tare da gudun Duniya, Musamman yanda sarakuna da masu mulki na kasashe suke yi masa kyaututtuka masu yawa, amma sai ya mika wannan kyautar lo kudin gidan marayu, makaranta ko wata cibiya da take yada Addinin Allah.

A halin yanzu, tun kusan watan July da ya gabata, Dr Zakir Naik bai koma kasar India ba, saboda tsira da Addininsa da rayuwarsa.

Duk da rashin zamansa a kasar, sun kara rattaba zargi a kansa cewa, yana tunzura matasa su shiga jihadi da kuma kungiyar ISIS dake kasar Iraq.

A ‘yan watannin nan yayi lectures kusan guda shida a kasar Malaysia, kasar da daga baya itama ta hana masa gabatar da lecture ko watsa karatuttukansa a kasar.

A yanzu haka, wata kungiya mai suna HINDRAF, ta sako kasar Malaysia a gaba akan ta sauke shedar zama a kasar da ta bawa Dr Zakir Naik, Kuma ya sallamashi zuwa kasar India don tsareshi da hukuntashi.

Alhamdu Lillah, Shugaba Datuk Seri Anwar Ibrahim, yayi watsi da wannan korafin ta hanyar shawarar Prime Minister Dr Muhathir Muhammad (Kamar yanda wata Jarida a kasar Malaysia ta wallafa watannin baya) kuma ya hukunta zai narshi a kasarsa jar zuwa lokacin da zargin da ake masa zai tabbata.

A Kwankin Nan Dr Naik yana cewa: Babban abin takaici da bakin cikinsa shine hidima da aikin da yaci shekaru 25 yana yi, domin cigaban Musulunci, a yau rana tsaka ake nema a rusa.

Kuma, wannan shine salo da maqiya Addinin Musulunci da masu  goya musu baya suka ‘dauka wurin fada da duk wani Musulmi mai kishi.

Don haka wajibine mu sanya shi cikin addu’o’inmu.
Allah Madaukaki yana cewa:
(Abin sani kawai Muminai ‘yan juna juna ne).

Allah ya kare shi ya karfafe shi ya cigaba da sanya albarka a Da’awar sa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.