Labaran Yammacin Lahadi 10/11/2019CE – 12/03/1441AH. Cikakkun labaran

Labaran Yammacin Lahadi 10/11/2019CE – 12/03/1441AH. Cikakkun labaran

Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II ya daura laifin sace yaran Kano ga iyayensu.

Rufe boda: Karamin ministan gona, Mustapha Baba Shehuri ya ce nan gaba Najeriya za ta amfana.

Jami’an ‘yansanda a jihar Ogun sun kama wasu manoma da buhunan taban wiwi 42.

An kama wata mata a filin jirgin saman Aminu Kano da jariri dan watannin 6 da ake zargin ta sato shi ne.

Iran ta soke izinin da ta ba wata jami’ar hukumar da ke binciken ayyukanta na samar da makamashin nukiliya (IAEA) .

Wutar daji a wurare fiye da 100 sun raba dubban mutane da muhallansu a Australia.

Masu kada kuri’a miliyan 37 ne suka fita domin zaben ‘yan majalisun tarayya 350 da sanatoci 208 a Spain.

EPL: Manchester United ta ci Brighton & Hove Albion 3:1 a wasan yau.

EPL: Wolverhampton ta ci Aston Villa 2:1 a wasan jiya.

Arsenal ta fara tattaunawa da tsohon mai horar da Barcelona Luis Enrique don duba yiwuwar maye gurbin Unai Emery.

*By Musa Rayuwa Jibia*

Leave a Reply

Your email address will not be published.