HAKKOKIN GUDA 6 NA ZAMAN KAN HANYA A MUSULINCI (HAKOKIN MASU ZAMA A MAJALISSA)

#HAKKOKIN GUDA 6 NA ZAMAN KAN HANYA A  MUSULINCI (HAKOKIN MASU ZAMA A MAJALISSA)

Daga Adhã’a bn Yasaar daga Abi Saeedul Khudiry R.A daga Manzon Allah SAW yace;
*(Ina yi maku kashedi akan zama akan hanyoyi)* sai Sahabbai sukace ai Manzon Allah SAW bakomai muke ba gurin hirar mune da hutawarmu,sai yace;
*(To idan ya kama dole sai kun zauna to ku baima hanya hakkinta)*sai sukace wadannene hakkokin zama akan hanya?? Sai yace;
*(Kamewa daga Kallon haramun,kamewa daga cutarwa da mayar da Sallama da Umarnin da abu mai kyau da hani daga abu marar kyau)*
@ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺃﺣﻤﺪ 3/36 ‏( 11329 ‏)ﺍﻟﺒُﺨَﺎﺭِﻱ 3/173 ‏( 2465 ‏)ﻣﺴﻠﻢ 6/165 ‏( 5614 ‏) ﻭ 7/2 ‏( 5699‏)

#HAKKI NA FARKO
*1-Rumtse idanu*
Wato yana cikin hakkin wajibi akan dukkan wanda zai zauna akan hanya to wajibine ya kame ganinsa daga kallon rahamun,matukar bazai kameba to zama a wannan waje haramunne domin dukkan wata hanya da take kai mutum zuwa ga haramun to bin wannan hanyar haramunne.
Kamewa daga kallon mutane ya hada kallon maza da na mata domin yawan kallon mutum koda namijine batare da wani dalili yana cutar da mutum cutar da mutum kuma haramunne.

#HAKKI NA BIYU
*2-Kamewa daga cutar da mutane da sauran halittua*

Kada wajan zamanku ya zama center ne na hada fada da gulma da yi da mutane da cutar da al’umma to wannan wajan zaman haramunne zama acikinsa.

Manzon Allah SAW yace:
*(Musulmi shine wanda dukkan musulmai suka kubuta daga cutarwarsa ta harshensa da hannunsa)*

#HAKKI NA UKKU
*3-Mayar da Sallama da amsa tambaya*

Yin sallama mustahabbine amsawa wajibe sannan wanda yake tafiya shine zai farawa na zaune sallama sai kuma shi na zaunen wajibine ya amsa sallamar wannan mai sallamar.

Dukkan wajan zaman da ba’a amsa sallamar mutane ko sai dai a amsa sallamar wanda ake so aka sami amma wanda aka raina ko kallo bai isaba,zama a irin wannan waje haranunne.

Amsa Sallama da amsa gayyata da amsa tambaya hakkine na musulmi akan dan uwansa musulmi.

Manzon Allah SAW yace;
*(Abubuwa guda biyae wajibine ga musulmi akan dan uwansa,mayar da sallama,gaishe da mai Atishawa,amsa kira da tambaya,zuwa duba marar lafiya,da rakiyar gawa)*
@صحيح الجامع.

#HAKKI NA HUDU
*4-Wajibanci Umarnin da abu mai kyau da hani akan abu marar kyau*

Umarni da abu mai kyau da hani akan abu marar kyau shine babban abinda ya sanya Allah ya fifita wannan al’umma akan sauran dukkan al’ummomi.

Allah yana cewa;
{ﻛُﻨﺘُﻢ ﺧَﻴﺮَ ﺃُﻣَّﺔٍ ﺃُﺧﺮِﺟَﺖ ﻟِﻠﻨَّﺎﺱِ ﺗَﺄﻣُﺮُﻭﻥَ ﺑِﺎﻟﻤَﻌﺮُﻭﻑِ ﻭَﺗَﻨﻬَﻮﻥَ ﻋَﻦِ ﺍﻟﻤُﻨﻜَﺮِ ﻭَﺗُﺆﻣِﻨُﻮﻥَ ﺑِﺎﻟﻠﻪِ}
Dan haka wajibine akan dukkan wanda al’umma tana umarni da abu mai kyau tana hani akan abu marar kyau,ba sai malami kadai ba,kowa zaiyi hakanne gwargwanda iyawarsa.sannan wannan wajibanci yana kara karfi akan masu zama akan hanya.

Manzon Allah SAW yana cewa;
*(Dukkan wanda yaga abun ki to ya chanzasa da hannunsa idan bazai iyaba to da harshensa idan baya da ikon to yaki abin azuciyarsa wannan shine mafi raunin Imani)*.

#HAKKI NA BIYAR
*5-Wajan zaman ya zama gurine na tattauna alkhairi*

Allah yana cewa;-
(لَّاخَيْرَ فِي كَثِيرٍ مِّن نَّجْوَاهُمْ إِلَّا مَنْ أَمَرَ بِصَدَقَةٍ أَوْ مَعْرُوفٍ أَوْ إِصْلَاحٍ بَيْنَ النَّاسِ ۚ وَمَن يَفْعَلْ ذَٰلِكَ ابْتِغَاءَ مَرْضَاتِ اللَّهِ فَسَوْفَ نُؤْتِيهِ أَجْرًا عَظِيمًا)
@النساء (114)AnNisaa

*(Bãbu wani alhẽri a cikin mãsu yawa daga gãnawarsu fãce wanda ya yi umurni da wata sadaka kõ kuwa wani alhẽri kõ kuwa gyãra a tsakãnin mutãne. Wanda ya aikata haka dõmin nẽman yardõdin Allah to zã Mu bã shi lãda mai girma)*

Dukkan wajan da ba’a tattauna alkhairi sai sharri to wajibine mutum ya nisanci wajan wannan zama domin zama acikinsa haramunne.

#HAKKI NA SHIDA
*6-Dauke abin cutarwa daga kan hanya*

Yana cikin hakkin zama akan hanya dauke abin cutarwa daga kan hanya yin hakan yana cikin imani.

Manzon Allah SAW yana cewa;
*(Imani yana da reshe guda saba’in da wani abu,mafi falalar reshe shine fadar:ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ، mafi kankantarsa shine dauke abin cutarwa akan hanya,kunya wani yankine daga cikin imani)*
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ.

Dauke abin cutarwa daga kan hanya Sadakane kuma hanyace ta kai mutum zuwa aljanna.

Manzon Allah SAW yana cewa;
*(Kowace gaba ta dan Adam an dora mata aikin Sadaka a kowane yini,……kuma dauke abin cutarwa daga kan hanya sadakane)*
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﻭﻣﺴﻠﻢ.

Manzon Allah SAW yana cewa;
*(Wani mutum yana tafiya akan hanya sai yaga wata kaya da take cutar da mutane sai ya sareta sai Allah ya godewa Aikisa sai ya gafarta masa……)*
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﻭﻣﺴﻠﻢ.

Annabi SAW yana cewa;
*(Wani mutum da bai taba aikata wani alkhairi ko sau daya ba sai wata itaciyar kaya mai cutar da mutane,sai Allah ya godewa aikinsa ya sanyasa a aljanna)*
@رواه ﺃﺑﻲ ﺩﺍﻭﺩ

  Allah ne mafi sani

Allah bamu ikon sauki wannan hakkoki.

Leave a Reply

Your email address will not be published.