[[Ka karanta]] Whatsapp sun fidda sabon tsarin da aka jima ana jiran fitowarsa.

Whatsapp sun fidda sabon tsari da aketa jira.

Wannan matsala ita ce: yadda hotuna da audio da videos suke cika wayar mutane ba-gaira-ba-dalili, kawai kana bude data zakaga hotuna sun cika maka waya ba tareda ka downloading ba.

Wannan matsala ta addabi mutane sosai wanda har hakan yakan iya sa mutane su fita a cikin groups, da zaka tambayesu zasuce maka abubuwa ne suke cika musu waya, su kuma basu so.

Yadda za’a magance wannan matsala shine:
Bayan an bude whatsapp group
1. A danna wasu digo 3 dake hannun dama ta saman group
2. A zabi abinda ke farko wato “group information”
3. Abubuwa 3 zasu bayyana, sune mute notifications, custom notification da kuma media visibility.
4. A zabi media visibility
5. A zabi no
6. A karshe sai a danna OK

Daga nan hotuna ko videos bazasu shiga wayarka ba, amma zaka iya ganinsu a cikin group.

Wannan tsari ya takaita ne kawai a group, banda na contacts din mutum.

Taimaka ka sharing wa wasu domin suma su amfana.

Leave a Reply

Your email address will not be published.