[[Ka karanta]] Yawan ‘yan Nigeria sama da miliyan 60 ne basu iya karatu ko rubutu da kowane harshe.

Babban sakataren Hukumar kula da ilimantar da ‘yan kasa a Najeriya
*Farfesa Abba Abubakar Haladu*

A wani taro a birnin tarayyar kasar Abuja, ya bayyana cewa: fiye da ’yan Najeriya miliyan 60 ne ba sa iya rubutu da karatu cikin kowane yare.

Farfesan yace:  wannan ne dalilin rashin ci gaba da kasar ke fuskanta, duba da yawan manya da matasa da
wannan al’amari ya shafa.

Ya kara da cewa idan har ana bukatar kasar ta bunkasa a
fannoni da dama, dole ne dukkan mutanen kasar
su iya rubutu da karatu da kuma lissafi a ko ina
suke.

Shi kuma Ministan  ilimi na Nigeria
*Malam Adamu Adamu*

Yace wajibi ne a dauki matakan gaggawa don kawo sauyi ganin yadda yawan yaran dake barin makaranta ke karuwa.

*ASOF*

Wannan bincike da Hukumar iliman ta Nigeria tayi ya samo asali ne duba da yadda ilimin kasar ya lalace sai kaga dalibi ya gama primary ko secondary be iya karatu ko rubutu ba. Tambaya anan shine yaya rayuwar dalibin zata kasan ce idan yaci gaba da karatu a haka?
Na farko de karatun nasa baze ci gaba ba saboda  bashi da isheshen ilimi da ze iya ci gaba da karatun, shiyasa ake yawan fusakantar matsaloli musamman wajen rubuta jarrabawa ta JAMB.

Idan ana bukatar ingantaccen ilimi a kasar mu ta Nigeria ya  zama dole gomnati, malamai da iyaye su tashi tsaye dan ganin cewa an magance wannan matsala kafin ta shafi wadanda suke tasowa.

By Abdullahi Musa Usman Bade

Leave a Reply

Your email address will not be published.