[[Ka karanta]] Yadda ake rubuta CV (Curriculum vitae) na musamman

CV document ne dake dauke da muhimman bayanan mutum, kamar su profile, da wuraren da mutum yayi karatu da ire-iren kwali(qualifications) da ya samu da kuma wasu kwarewa da yake dasu a fannoni. 
*Me yasa nake submitting CV na a wurin neman aiki amma basu nema na domin Interview? 
Matsalar ita ce CV da ake rubutawa bata kai abinda ake cewa “30 seconds test”. Abinda ake nufi da “30 seconds test” shine, bayan shi wanda zaiyi maka interview ko zai baka aiki bayan 30 seconds da bibiyar CV naka. 
Abubuwanda da akeso da wadanda ba’a so yayi rubuta CV
1. Kada ka fara rubuta CV da Curriculum vitae. Ka fara rubuta sunanka da manya bakake a sama. 
2. Kayi kokari adireshin da kayi amfani dashi a CV naka ya kasance na kusa da inda ake neman ma’aikatan ne, misali idan ana neman ma’aikata a Gombe, yi kokari kayi amfani da adireshin Gombe. Idan ma baka zama a wurin, yi kokari ka samu wanda yake zama a wannan adireshin. 
3. Kada kayi amfani da email address da rashin da’a, misali [email protected] , daga nan ma zasu gane kai ba na gari bane. Idan son samu ne gmail dinka ya kasance da sunanka a jiki, misali [email protected]
4. Karkashin wajen saka ranar haihuwa da jaha da karamar hukuma maganar gaskiya ba dole bane. Idan shekarunda ake nema ka wuce wannan kawai ka cire ranar haihuwar koko ka rage. Abinda aka fi buqata shine kwarewa. 
5. Wurin saka qualifications, zaka iya cire lokacinda aka baka admission, saboda wasu zasu fara makaranta a 2004 sannan su kammala a 2010 alhali course din na shekaru 4 ne, ba lallai ne rlya zamto laifinsu ba, amma bazasu tambayeka me ya faru ba. Kawai cirewa shi yafi. 
6. Qualifications na kwarewa suma suna sa mutum ya rasa aiki, misali ana neman wadanda suka iya aikin computer, amma zaka tarar mutum ko taba kunna computer bai taba yi ba amma sai ya nema shima.  Idan kana aikin hidima wa kasa ne (corp member)  yi kokari ka samu wasu ilimomi domin karawa CV naka daraja. Hakama wadanda ke aiki, zasu iya cin moriyar ranakun da ba’a aiki domin samun ilimomi a wasu fannin. Hakan zai taimaka idan za’a nemi wani aikin. 
Idan kanada fannoni wadanda ka kware, ba duka ne zaka sa a CV ba, sai dai wadanda suka dace da fannin da ake neman ma’aikata. 
Wurin saka Hobbies da Interest, nan ma ana kuskure sosai, misali wani zaka ga ya saka playing video games ko football, haba Malam a wurin aikin zakayi musu wannan?  Abunda akeso a saka a wurin sun hada da: researching, meeting people,  playing scrabble ko chess, mentoring da kuma travelling. Kuma ka tabbatar abinda kasa hakan ne. 
9. Wurin saka referees ana buqatan suna, adireshi, lambar waya da kuma Gmail. Zaka iya amfani da danginku amma kada sunan mahaifinku ya kasance iri daya. Sannan referee din ya kasance yasan cewa kasa shi a cikin referees naka. 
10. CV ya kasance black and white, ana iya amfani da color ne a wurare guda biyu: na farko idan ana neman wadanda suke aikin graphic designer, koko idan kanada logon kamfanin da ka taba yin aiki a CV naka.
11. Kada ka forwarding CV naka zuwa mail na wadanda suke neman ma’aikata, ka shirya sabon saqo ka tura musu amma ba sharing ba. 
12. Ka tabbatar subject na mail dinka yana dauke da gurbi da kake nema na aiki. 
13. Kada ka saving CV naka a cikin Computer da “My CV” ko “Edited CV”, ya kamata ka saving da asalin sunanka, misali Murtada Dahiru Abubakar. 
14. Ba lallai kasa password naka akan CV ba sai idan ance asa. 
Da fatan kunji dadin wannan rubuta, zaku iya ajiye tsokaci ko gyara a wurin comment.

1 thought on “[[Ka karanta]] Yadda ake rubuta CV (Curriculum vitae) na musamman

Leave a Reply

Your email address will not be published.