[[JAMB 2020]] Meya Kamata Nayi Kafin Ranar Jarrabawar Jamb

*[Jamb]* *2020*

*Meya Kamata Nayi Kafin Ranar Jarrabawar Jamb*

Daga:ASOF*
_Ayayinda ake rijistar Jarabawar #Jamb Ya Kamata Dalibi Yasan Da Wannan:-_

Ka tabbatar da registration slip dinka yana hannunka sannan  kayi kofinsa kamar  guda biyu a hannunka.

1. Dalibi ya tabbatar yayi gwajin jarabawa a na’ura mai kwa-kwalwa musamman  ga dalibin da bai iya amfani da Computer ba.

2. Ka tabbatar da rana da kwanan watan da zakayi jarrabawar da lambar kujerar da zaka zauna.

3. Ka ziyarci cibiyar da aka turaka domin zana jarabawa ka tabbatar da yanki da take yanda ranar jarabawa zaka iya kai kanka kai tsaye ba tareda kwatance ba don gudun makara.

4. Ka tabbatar da lokacin da safe ne ko da yamma kuma karfe nawa ne? Mafi kyau ka kasance a Inda zakayi jarabawa kafin lokacin jarabawar domin tantancewa.

*Me Yakamata Nayi Aranar Jarabawa?*

1. Ka tanadi fensir, biro do kuma shafana.

2. Ka halarci cibiyar da zakayi jarabawar akan lokaci.

3. Kabi dukkan sharudai da ka’idojin da za’a gabatar muku a wajen.

4. Ka tabbatar an tantanceka kafin  jarabawar da kuma lokacin kammala jarabawar.

5. Kada ka dannna Computer har sai an bada umarni.

6. Ka nustu sosai wajen amsa jarabawar don gudun rikicewa a yayin jarabawa.

7. Kada kayi “Refresh” din Computer ko ka danna “Submit” har sai ka kammala jarabawa.

*_Mu hadu a darasi na gaba domin sanin yarda zakayi amfani da keyboard domin gudanar da Jarabawa_*

By Aliyu Miko
@ASOF 2020

Leave a Reply

Your email address will not be published.