KUNGIYAR IZALA TA TAYA GWAMNAN JIHAR BAUCHI MURNAR SAMUN NASARA A KOTUN KOLI

*KUNGIYAR IZALA TA TAYA GWAMNAN JIHAR BAUCHI MURNAR SAMUN NASARA A KOTUN KOLI*

A yammacin yau Juma’a ne Kungiyar Izala reshen jihar Bauchi takai ziyarar taya gwamnan jihar *Sen Bala A. Muhammad* murnar samun nasara a kotin koli bisa shari’ar data gudana tsakaninshi da tsohon gwamnan jihar.

Da yake jawabi yayin ziyarar, shugaban Kungiyar na jiha *Alh. Muhammadu Inuwa Dan’asabe* ya shaidawa gwamnar cewa dalilin kawo wannan ziyara shine mu tayaka murnar wannan nasara daka samu sannan mu tunatar dakai nauyin daya rataya a wuyarka na jagorantar al’umnar jihar Bauchi. Sannan shugaban ya kara da cewa a kullum suna cikin addu’o’i na fatan alkhairi ga wannan jiha domin ganin komai yana tafiya yadda ya kamata.

Shima a nashi bangaren, mai Girma Gwamnan jihar Bauchi Sen. Bala A. Muhd ya nuna matukar farin cikinsa ga wannan kungiya bisa goyon baya da addu’o’in da suke masu tun hawansa kan karagar mulki a wannan jiha. Sannan yasha alwashin cika alakawurran daya dauka wa al’ummar jihar Bauchi inda ya shaidawa tawagar cewa ya dauki alkawarin fara biyan mafi karancin albashi nan take ga ma’aikatan jihar kuma zai debi ma’aikata domin rage rashin aikinyi ga matasa. Ya kuma jaddada bukatar yi masa nasiha a asirce a duk lokacin da bukatar hakan ta taso, inda yace idan sai al’amari ya faskara tukunna aje kan mumbari.

Daga karshe, Imam Babangida Sulaiman shine ya rufe da addu’a inda gabannin haka yayi wa’azi mai ratsa zuciya ga mai girma gwamna da sauran yan tawagarsa.

JIBWIS SOCIAL MEDIA
BAUCHI STATE DIRECTORATE
24/01/2020

Leave a Reply

Your email address will not be published.