sabbin mutane 26 sun kamu da cutar covid-19 a kano jiya Lahadi
Hukumar dakile cututtuka masu yaduwa NCDC da Ma’aikatar Lafiya ta jahar kano sun sanar da samun Karin mutune 26 masu dauke da cutar Corona wato Covid-19 a Jihar Kano.
Wannan tasa adadin wadanda suka kamu da cutar a jihar Kano yanzu ya kama mutum 602 sannan kuma mutum 26 daga ciki sun rasu, sannan mutune 50 sun warke kuma an sallame su.