Ganduje ya ce Cutar Covid-19 ta Shafi, Addinin mu, Mu’amalar mu, Tattalin arzikin mu, ta shafi dukka alamurorin mu na rayuwa

Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar ganduje ya ce Cutar Covid-19 ta Shafi, Addinin mu, Mu’amalar mu, Tattalin arzikin mu, ta shafi dukka alamurorin mu na rayuwa 

Ya Kara da cewa: Yau Duniya dukka a kulle take ba kamar yadda aka saba ba al’amari irin wannan ba, sai dai mu cigaba da rokan Allah ya dauke wañnan cuta.
Shirye-shiryen da gwamnati takeyi shine; shine ana daukar samfur na Al’umma wadan da akaga alamomi suna dauke da wannan cuta.
Wadan da aka samu suna dauke da wanna cuta munyi tanadin guraren ajjiye su, guraren kwana masu kyau, duk da dai komai kyan guri ga mara lafiya ba mai kyau bane, inji Ganduje.
Ya kara da cewa: munyi tanadin wadan da suke jira ko sun kamu da wanna cuta ko kuma akasin hakan, to mun tanadi babban Hotal domin su, idan baka da wanna ciwo sai ka koma gida, idan kuma kana da cutar sai mu kai ka Inda zaka zauna a kula dakai abaka kulawa da magungunan da aka tanada,  Wadan da zasu kara karfi na jikin ka har kuma a samu sauki” 
Idan kuma abun ya baci sosai akwai wani asibitin daban inda za’asa masa na’urori. 
Cutar Coronavirus dama ciwo ne mai bada matsalar numfashi za’asa na’urori wadan da zasu taimakawa mara lafiya yayi numfashi sosai.
Tun daga kan Sarakuna, Hakimai, Dakatai, Masu unguwanni, Limamai Da malamai  kowa ya fahimci wannan cuta Alhaki ne da ya rataya akan mu, kuma babban matsalar shine kana da wanna cuta Kai daka shafa masa baka sani ba, kuma shima da ya dau wanna ciwon bai sani ba.
Shi yasa aka bude guraren daukar samfur-samfur domin adun ga aunasu to wanna yana da mahimman ci sosai da sosai.
Gwamnan Jahar Kano yayi wannan jawabin ne a gurin taron karawa juna sani da ya hada akan cutar a fadar gwamnatin sa inda aka tara sarakunan Jahar Guda 5 da kuma sauran Jami’an Gwamnati da masu ruwa da tsaki.
A Jawabin mai martaba Sarkin kano Yace: Dole ne mu yabawa gwamnati da irin kokarin da take tun kafin wannan cutar ta shigo wanna jaha.
Tabbas ba abune boyayye ba, gudunwar da gwamna ya bayar musamman a wajen tausa sawa al’umma da aka kafa kwamiti da ya samu gudummawa daga ban garori daban-daban inda hakiman mu suke rabawa ga talakawa, Kuma muna samun rahoton abun da akeyi muma kuma muna bada rahotan abun da ake yi.
Muna yiwa gwamna godiya amadadin al’umma domin dukkanin mutane sun aminta cewa an raba wdannnan kayayyaki a tsabtace. 
Sai dai Al’ada ta dan adam ba’a rasa kurakurai a dukkan al’amura na rayuwa. 
Abun da dai kawai zamu kara jadda dawa shine ana bukatar a kara wannan taimako, sannan muna godewa dukkanin wadan da suka tara wannan taimako a wanna fanni na taimakawa al’umma.
Alhaji Aminu Alhassan Dantata, Alhaji Abdussamad Bua, Alhaji Aliko Dangote, Alhaji Isyaka Rabi’u da sauran wayan da suka bada iko suka taimaka muna gode musu Allah yabasu ladan da yai al’kawari zai bawa masu irin wanna taimako, Allah ya sakamu acikin ladan baki daya. Inji Maimartaba Aminu Ado.
Ya kara da cewa: Al’umma baki daya muna kara kira garesu dasu yadda cewa wannan cuta gaskiya ce, subi dokoki na gwamnati da dabarurrukan da ma’ai katan lafiya suka Sanar damu domin mu gudu tare mu tsira tare, musamman wajen jawo hankali wajen tsabtace jiki da yanke handuwa duk da dai cewa wannan ya zam ruwan dare a gurin al’umma.
Al’umma sun aminta da wanna takunkumin na rufe fuska, Alhamdulillahi ya zama wajubi mu yabawa gwamnati da irin kokarin da take na abun da ake rufe hanci da baki dan kiyaye al’ummar mu da rayukan mu baki daya.
Muna kira ga dukkannin wayannan abu buwa da akeyi mu tunatar da kanmu cewa Ubangiji shine abun roko a cikin wanna al’amura da muke fuskan ta.
Sarkin Yayi kira da mu yawai ta Istigfari ga Ubangiji, Mu cigaba da yin salati ga fiyayyaen Halitta Annabi Muhammad (SAW).

Leave a Reply

Your email address will not be published.