Ganduje ya tattauna da sarakunan kano domin magance cutar covid-19

Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya gana da Sarakunan yanka su 5 masu daraja ta daya na jihar Kano da suka hada da Sarkin Kano kuma shugaban majalisar Sarakunan Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero da Sarkin Rano Alhaji Muhammad Inuwa Kabir da Sarkin Karaye Alhaji Ibrahim Abubakar II da kuma Sarkin Gaya Alhaji Ibrahim Abdulqadir Gaya domin tattaunawa akan cutar Corona wato Covid-19 da kuma rawar da masaratun jihar Kano gaba daya zasu taka wajen ganin an dakile cutar.

Gwamna Ganduje na tare da Mataimakin sa Dr Nasiru Yusuf Gawuna da Sakataren Gwamnatin jiha Alhaji Usman Alhaji da Kwamishinoni da sauran yan kwamitin kar ta kwana na Covid-19 na jihar Kano da sauran hakimai da masu ruwa da tsaki a harkar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.