Jigawa ta bada izinin cigaba da sallar juma’a yayin da mutane 7 suka warke daga cutar covid-19


Jigawa ta bada izinin cigaba da sallar juma'a yayin da mutane 7 suka warke daga cutar covid-19

Gwamnan jihar jigawa Alh Badaru Abubakar ya shaidawa manema labarai a dutse cewa mutane 7 sun warke daga cutar covid-19 kuma an sallame daga gurin killace masu dauke da cutar ta covid-19

Gwamnan ya ce mutane 118 suka kamu da cutar a fadin jahar yayin da mutane biyu suka rasu.

Gwamna Badaru ya CE kashi %53 na masu dauke da cutar a jahar Almajiran da gwamnatin Kano ta mayarwa jigawa ne.

Bayan ganawar gwamnan da kungiyar malamai ta jahar jigawa, ya amince da acigaba da yin sallar juma'a, tare da daukar matakan kare kare kai daga daukar cutar covid-19

Daga cikin matakan akwai bada tazara a cikin masallaci da kuma wanke hannun Kafin shiga masallatan

1 thought on “Jigawa ta bada izinin cigaba da sallar juma’a yayin da mutane 7 suka warke daga cutar covid-19

Leave a Reply

Your email address will not be published.