Sabbin mutane 27 sun kamu da cutar covid-19 a kano

Hukumar dakile cututtuka masu yaduwa NCDC da Ma’aikatar lafiya ta jahar kano sun sanar da samun Karin sabbin mutune 27 masu dauke da cutar Coronavirus wato Covid-19 a Jihar Kano.

 Wannan ta sa adadin wanda suka kamu da cutar a jihar Kano yanzu ya kama mutum 693 sannan kuma mutum 33 daga ciki sun rasu, sannan mutum 74 sun warke kuma an sallame su.

Leave a Reply

Your email address will not be published.