Za acigaba da yi sallar juma’a a zamfara


Za acigaba da yi sallar juma'a a zamfara

Gwamnan jahar zamfara Muhammad Bello Matawalle ya bayyana bude masallatan juma'a Dana kamsus salawatu da kuma maja mi'u domin cigaba da ibadu da rokon Ubangibi ya ya ye annobar cutar covid-19 a fadin jahar. Za'a bude masallatan ne Bayan kiraye kiraye daga malaman addini da kungiyoyin fararen hula da dai dai kun mutane. Gwamna Matawalle ya ce wannan wata Dama ce ga al'ummah domin rokon Allah yakawo dauki kan wannan cuta ta coronavirus. Daraktan ya da labaran fadar gwamnatin jahar Zamfara Yusif Idris Gusau, ya ce gwamnan ne ya bada izinin bude masallatan tacikin wani shiri da yayi a kafar yada labarai ta jahar Zamfara, inda yace dukkan masallatai yanzu za'a cigaba da gudanar da sallah, amma banda sallar tahajjudi da sallar tarawi, sannan kuma ya ce masallatai zasuyi kokari wajen bayar da tazara a lokacin salloli. Sannan an bada umarni a wasu gurare aje kasuwanni ayi siyayya, amma ASA takum kumin rufe bani da hanci, tare da bada tazara tsakanin al'umma. Wadannan sune kadan daga cikin umarnin da mai girma Gwamna yaba yar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.